Posts

Showing posts from November, 2017

A CIGABA DA TARON WAYAR DA KAN AL'UMMA DA KUNGIYAR MATASAN ZMF TA TSAKIYA KE GUDANARWA A SASSA DABAN DABAN NA YANKIN ZMF TA TSAKIYA

Image
____________________________________ Kungiyar ta gana da alummar yankin mayanchi dake karamar mulki ta maru, Wanda taron ya gudana a fadar  uban kasar mayanchi . Shugaban kungiyar Rufai bala ub ya bayyana Masu ayukkan kungiyar tareda bayyana Masu cewa Yana daga cikin manufofin wannan kungiyar Samar da shugabanci na gari. A nashi jawabin comrade Nura bello Dan kishin kasa ya bayyana cewa matasa sune wadanda ke taimakawa wajen kawo cigaba Mai dorewa. Darektan walwala da jin dadi ya bayyana cewa yanzu lokaci Yayi da yakamata abaiwa zamfara ta tsakiya damar rike kujerar gwamna laakari da yadda wannan yankin ya jajirce wajen taimakawa sauran yankuna, kuma ya zayyano dukkanin Masu neman kujerar gwamna daga wannan yanki. Wani  daga cikin mahalarta taron ya nemi kungiyar matasan zamfara ta tsakiya akan tayi Kira ga hukumar INEC akan ta Kara fadada wuraren karbar Katin zabe, Sakataren uban kasar mayanchi Yayi tambaya akan yadda ake shiga wannan kungiyar. Shi kuma wani Ya...

Zaben 2019: Gwamnatin Buhari Tana Barazana Ga Hadin Kan Kasa – Inji Atiku

Image
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a matsayin babban barazana ga hadin kan kasa, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito. Majiyar mu ta tattara cewa Atiku ya rubuta wasika zuwa ga jam’iyyar APC, inda yake sanar da su shawararsa na ficewa daga jam’iyyar. Ko da yake ya rubuta wannan wasiƙar ne a ranar 18 ga Oktoba, 2017, amma shugaban jam’iyya mai mulki ta APC a ranar Juma’a ya karyata karbar wannan sanarwa daga tsohon mataimakin shugaban. A cikin wasikar, Atiku ya ce shawar ficewa daga jam’iyyar bai kasance game da shi ba, amma game da makomar kasar Najeriya. “Na gagara fahimtar rashin aikin wannan gwamnatin jam’iyya mai mulki, musamman ma game da yadda al’amuran mutanen mu ke ta barbarewa ta hanyar kabilanci da addini wanda ke barazana ga hadin kanmu fiye da kowane lokaci a cikin ‘yan kwanan nan da kuma kalubale da al’ummar kasar ke fuskanta sakamakon durkushewar tattalin arziki”, in ji shi. A cikin wasikar wanda U...

Buhari Ya Biya Kudin Makaranta Miliyan 164.8 Na ‘Yan Matan Chibok 106

Image
Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya amince da biyan kuɗin dalibai na jami’a na ‘yan matan Chibok 106, fadar shugaban kasa a ranar Lahadi 26 ga watan Nuwamba ta sanar da hakan. Mataimakin shugaban kasa a kan shafukan yanar gizo Lauretta Onochie ta tabbatar da hakan a shafinta ta Twitter a ranar Lahadi. Ta ce ‘yan matan suna karatu ne a jami’ar Amurka ta Najeriya wanda ke garin Yola, jihar Adamawa, wanda tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya kafa. Majiyar mu  ruwaito kwanan nan cewa iyayen sauran ‘yan makaranta na Chibok sun nuna bakin ciki ga shugaba Buhari game da makomar’ ya’yansu wadanda har yanzu suna hannun Boko Haram. Iyaye, a cikin wata wasika da suka rubuta wa shugaba Buhari, sun bayyana cewa kimanin iyaye 20 daga cikinsu sun mutu yayin da suke jiran dawowar ‘ya’yansu. Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin cewa, sauran ‘yan matan za su samu ‘yanci bayan masu tayar da kayar baya sun saki ‘yan mata 82 bayan musanya da wasu mayakan Boko Haram. Bayan watan...

Batan-Baka-Tan-Tan: Jam’Iyyar PDP Ta Sarewa Atiku Gwiwa Game Da Batun Takarar Sa A 2019

Image
Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta yi tsokaci a game da batun ficewa daga jam’iyyar APC da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma fitaccen dan siyasa, Alhaji Atiku Abubakar inda ta bayyana shi a matsayin wani mai ‘yanci a yanzu. Sai dai kuma jam’iyyar a cikin wani zance mai kama da na sare gwiwa, ta bayyana cewa tikitin ta na takara a zaben 2019 mai zuwa ba na kowa bane don haka ba zai same shi ba hakanan kai tsaye sai yayi takarar neman sa. Majiyar mu, dai ta samu cewa a cikin sanarwar da jam’iyyar ta PDP ta fitar, ta bayyana cewa hakika Allah ne ya nufi tsohon mataimakin shugaban kasar da shiriya shine babban dalilin da yasa ya fita yabar jam’iyyar. Daga nan ne kuma sai jam’iyyar ta mika sakon gayyata ga duk wanda yake ganin ba’a yi masa adalci a jam’iyyar ta APC da ya garzayo a jam’iyyar tasu domin su jam’iyyar su jam’iyya ce mai adalci ga kowa.

Shugaba Buhari Ya Zagaye Kansa Da Mahandama – Sanata Shehu Sani

Image
Sanatan yayi wannan ikirarin ne a yayin wata fira da yayi a gidan rediyon RAVE FM a garin Osogbo lokacin da yake gabatar da wata kasida tare da sharhi game da yadda gwamnatin nan ke yakar cin hanci da rashawa. Majiyar mu, dai ta samu cewa Sanata Shehu ya jaddada cewa baya shakku to tababar yakinin shugaba Buhari wajen yin yaki da rashawa tun daga zuciyar sa amma tabbas ya san na zagaye dashi hakan bai kai zuciyar su ba. Daga nan ne ma dai sai ya shawarci ‘yan kasa dukkan su da su dukufa wajen yiwa shugaban addu’ar Allah ya kubutar dashi daga hannun su.

Gusau: Zamfara Ta Sami Sabuwar Kwamishinan ‘Yan Sanda

Image
Sabon kwamishinan ‘yan sanda na jihar Zamfara, Mista Kenneth Ebrimson ya fara aiki. Ebrimson, ya kasance daga sashin ayyuka na musamman a hedkwatar hukumar ‘yan sanda kuma ya maye gurbin tsohon kwamishina, Alhaji Shaba Alkali wanda aka sake dawo da shi a hedkwatar da ke birnin Abuja. Sanarwar da jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar Zamfara, DSP Muhammad Shehu, ya bayar a ranar Juma’a, 24 ga watan Nuwamba, ta nuna cewa sabon kwamishinan ‘yan sandan ya ziyarci wuraren da ake rikici nan da nan don tsara yadda za a magance matsalolin yankin. Hukumar ‘yan sanda Ya ce, “Mun ziyarci yankin karamar hukumar Shinkafi daya daga cikin kananan hukumomin da ‘yan bindigar da ba a sani ba, suka kai hari a makon jiya”. Ya ce sabon kwamishinan ya yi ziyarar ta’aziyya zuwa ga sarkin Shinkafi, Alhaji Muhammad-Makwashe Isah, game da hare-haren kwanan nan da kuma rasa rayuka, ya kuma kira ga goyon baya da hadin kai daga masarautar. Kwamishinan, wanda ya sadu da shugabanni al’u...

Harin Masallaci Yayin Sallar Juma’A Yayi Sanadiyar Mutuwar Mutum 54 A Masar

Image
'Yan bindigar sun bude wuta a kan jama’a ne a wani masallaci dake arewacin yankin Sinai a kasar ta Masar. Harin masallaci yayin sallar juma’a ya yi sanadiyar mutuwar mutum 54 a Masar Hakazalika gidan talabijin din ya ce fiye da mutane 75 sun samu raunuka. Ana cigaba da kokarin ceto mutanen da harin ya ritsa da su a masallacin. Zamu kawo ma ku karin bayani a kan Hari da zarar mun samu karin rahotanni daga majiyar mu. Ana samun yawaitar kai hare-hare a wuraren ibada domin idan ba ku mance ba ko cikin satinnan mai karewa saida wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan masallata a wani masallaci dake Garin Mubi ta jihar Adamawa.

WANI BABBAN JIGON SIYASAR SOCIAL MEDIA NA PDP YA ZIYARCE NI A YAU JUMA'A 24/11/2017>>>>/03:15PM,

Image
Assalamu Alaikum. ----------------------------------------------------------- Wani jigo kuma dan gwaggwarmayar siyasa a Jam'iyar PDP  (Comrade Dan Autan Belmat Matawallen Maradun)a yau ya kawomin ziyara ta musamman a nan masana'antata inda muke kasuwancin Apple wato (Apples Business Center Gusau) shakka  babu wannan ziyarar ta samu armashi sosai, kuma mun tattauna akan abubuwa mabanbanta, Don dabbaqa dankon zumunci. Ina adda'ar Allah ya mai dakai gida lafiya, kuma Allah ya taimaka! (SIYASA BADA GABA BA)

Kimanin Mutane 40,000 Neke Neman Aikin Malanta A Jihar Kaduna

Image
A jiya Alhamis ne Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa kimanin mutane 40,000 suka mika takardun su ne neman aikin malanta a makarantun gwamnati da ke Jihar. Gwamnan ya fadi wannan maganan ne kwanaki kadan bayan ya bayyana cewa gwamnatin sa zata sallami malamai makarantun firmare guda 21,780 wanda suka fadi jarabawar cacanta aiki da gwamnatin Jihar ta gudanar. Kimanin mutane 40,000 ne ke neman aikin malanta a Jihar Kaduna Hakan ne yasa gwamnatin Jihar tace zata maye gurbin malaman da zata sallama duk da cewa hakan bai yiwa mutane da yawa dadi ba har ma da kungiyar kwadigo na Jihar wanda ta jagoranci zanga-zangar lumana na nuna kin amincewa da sallamar malaman da gwamnatin Jihar ke niyyar yi. Wata sanarwa da ta fito daga mai baiwa gwamnan Jihar Kaduna shawara kan kafafen yada labarai, Samuel Aruwan tace gwamnan ya bayyana adaddin masu neman aikin ne yayinda yake ganawa da ‘Yan Majalisar Tarayyah a Abuja a ranar Laraba. Sanarwan ta cigaba da cewa El-Rufai ya ro...

Wani Saurayi Daga Najeriya Ya Zama Gwani A Wajen Gasar Rubutu,

Image
Yanzu haka an samu wani Matashi daga Yankin Arewacin Najeriya da yayi zarra a Gasar rubuce-rubuce da aka yi na tsawon rabin shekara a Najeriya da kuma Kasar Kamaru. Sada daga Garin Malumfashi ya samu damar zuwa Turai Wani gasa ne da aka fara tun tsakiyar shekarar nan a Garin Limbe na Kasar Kamaru wanda a karshe Sada ya zo na daya kwanan nan a Garin Abeokuta cikin mutane kusan 10. An hora wadanda su ka shiga gasar na wata da watanni inda a karshe aka zabi wanda yayi zarra. Bayan an dauki dogon lokaci ne dai Sada ya ciri tuta inda ya zo na farko a Najeriya. Hakan ta ba Matashin marubucin damar zama a Kasar Jamus na watanni 3 a karkashin gidauniyar Sylt ta Turai kamar yadda mu ka samu labari. An kuma zabi wanda yayi nasara daga Kamaru. Malam Sada Malumfashi yana zama ne a Garin Kaduna amma asalin mutumin Kudancin Jihar Katsina ne. Ko da dai Sada ya karanta ilmin sarrafa magunguna ne a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya ya koma fagen rubuce-rubuce kamar mahaifin sa Farfesa Ibrahim M...

Wasu Manyan ‘Yan Siyasar Jihar Adamawa Su Biyu Sunyi Sa-in-sa Akan Kai Kayan Agaji

Image
Lamarin dake kama da wasan kwaikwayo ya faru ne a babban filin jirgin sama na kasa da kasa dake Yola babban birnin jihar Adamawa, a lokacin da tawagar hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA ke shirin kai kayayyakin tallafi ga al’ummar Madagali, da rikicin Boko Haram ya shafa. Bayanai na nuna cewa dan majalisar wakilai dake wakiltar al’ummomin yankin Michika da Madagali, Adamu Kamale ya nemi ya bi jirgin tawagar hukumar bada agajin NEMA mai saukar ungulu, to amma sai dan majalisar dattawa mai wakiltar Adamawa ta tsakiya Senata Abdul’Aziz Nyako, wanda ke zama shugaban kwamitin aiki da cikawa na majalisar kuma mai sa ido kan harkokin hukumar NEMA, ya ce dan majalisar wakilan ya sauka saboda babu sunansa a jerin wadanda zasu kai kayayyakin tallafin, batun da ya harzuka dan majalisar. A wata takardar koke da ya rabawa manema labarai a Yola, dan majalisar ya zargi Sanata Abdul’Aziz Nyako da cin zarafinsa, da kuma hana shi sa ido game da kayayyakin da za a kai mazabarsa, abin d...

Na nazarci list din N-POWER Na bana da aka fitar talatar da ta gabata.

Image
Gaskiya akwai gagarumar matsala, ya kamata masu fada aji suyi wani abu akai. Zakaji matukar takaici in ka duba list din, zaka ci karo da kusan 5 pages baka ga sunan Musulmi ko daya ba, wasu pages din kuma bai fi ka samu mutum biyu ko uku ba. Bana jin al'ummar mu sun kai 5% a list din, 95% duk kiristoci ne. Don Allah duk wanda ke da iko ko fada aji, ko kuma Isar wa masu fada aji, ayi kokarin sanar dash halin da ake ciki don kwatowa al'ummarmu hakkin ta.

Za a Yiwa Malaman Makaranta Jarrabawa A Jihar Bayelsa

Image
Yanzu haka ana shirin yi wa Malaman Makarantun Firamare da Sakandare gwaji a Jihar Bayelsa kamar yadda mu ka samu labari a jiya. Gwamna Dickson zai fito da jarrabawar Malaman Makaranta Gwamnan Jihar Bayelsa Seriake Dickson ya bayyana cewa za a yi wa Malaman Makaranta jarrabawa a fadin Jihar kuma za a kawo wani kudiri a Majalisar dokokin Jihar da zai sa a rika yi wa Malaman Jihar irin wannan jarrabaw. Dole dai kowane Malami sai ya rubuta wannan jarrabawa inji Gwamna Dickson inda yayi wannan jawabi ta bakin mai magana da yawun sa watau Francis Agbo a jiya Laraba wajen wani taro da aka yi a Babban Birnin Jihar na Yenagoa. Agbo yake cewa Majalisar dokokin Jihar Bayelsa na nan tafe da wani kudiri da zai sa a rika yi wa Malaman Makarantun Firamare da Sakandare jarrabawa kafin a dauke su aiki domin ganin an gyara harkar Malanta a fadin Jihar.

Zimbabwe: Za’A Rantsar Da Emmerson Mnangagwa A Zaman Shugaban Kasa

Image
Magoya bayan Emmerson Mnangagwa suke rike da hotons a suna murna. Kakakin majalisar dokokin kasar Jacob Metunda ne ya bada sanarwar haka Laraban nan. Kakakin majalisar dokokin Zimbabwe Jacob Mudenda, ya ce za’a rantsar da Emmerson Mnangagwa, a zaman shugaban kasar ranar Jumma’a, biyo bayan murabus na Robert Mugabe, mutumin da ya juma yana mulkin kasar,al’amari da ya auku jiya talata. Sanarwar da kakakin majalisar ya bayar a yau Laraba, tana zuwa ne a dai dai lokacinda Mnangagwa yake shirin komawas kasar. Haka kwatsam tsohon mataimakin shugaban ya gudu daga kasar a ranar shida ga watan nan, bayan da Mugabe ya kore shi daga kan mukaminsa. Masu motoci sun yi ta busa kahon motocin su yayinda ‘yan kasar suke ta raye raye, da masu rangwada a Harare, babban birnin kasar don murnar murabsu din Mugabe, da ya bayyana jiya Talata, a cikin wasikar da kakakin majalisar Mudenda ya karanta a zauren majalisar.

Najeriya Ce Kan Gaba Wajen Samar Da Iri Na Noma A Yankin Afirka Ta Yamma – NASC

Image
Shugaban cibiyar samar da iri na noma ta NASC (National Agricultural Seeds Council), Mista Philip O. Ojo, ya bayyana cewa, kasar Najeriya ce ke samar da kashi 75 na iri na noma da ake amfani da shi a gaba daya yankin Afirka ta Yamma, wanda hakan ya maishe da kasar kan gaba wajen samar da iri na noma a yankin. Mista Philip ya bayyana hakan ne yayin da ya jagoranci tawagar cibiyar da ta ziyarci gwamnan jihar Jigawa Alhaji Badaru Abubakar, a ranar Litinin din da ta gabata. Shugaban cibiyar ya bayar da jawabi da cewar, “kasar Najeriya ce ka samar da kaso 75 na irin shuka da ake amfani da shi a yankin Afirka ta Yamma, wanda hakan ya maishe da ita kan gaba wajen fitar da iri zuwa kasashen ketare dake nahiyyar. Najeriya ce kan gaba wajen samar da iri na noma a yankin Afirka ta Yamma – NASC “Wannan shine bigire da kasar ta yi fintikau, amma muna bukatar ta kara hobbasa yinkurin ta. Sai dai irin taimako da gudunmawa da wasu jihohin kasar suke bayar wa abin yabawa ne, kuma muna kyautat...

Dalilin Da Yasa Har Yanzu Ana Damawa Da Tinubu A Siyasar Najeriya – Inji Sarkin Legas

Image
Oba na Legas, Rilwan Akiolu ya bayyana dalilin da yasa jigon jam’iyya mai mulki ta APC, Bola Tinubu, har yanzu yana da matsayi a harkokin siyasa a Najeriya. Sarkin ya ce takunsa ya sanya shi tsawon lokaci a siyasar Najeriya Najeriya. Da yake jawabi a Ibadan, babban birnin jihar Oyo a ranar Talata, 21 ga watan Nuwamba, Akiolu ya ce, “Jarumtakar Tinubu ya sanya shi a matsayin da yake a yau a lokacin da babban jam’iyyar adawa ta PDP ta matsa wa yankin kudu maso yammacin kasar lamba”. Oba na Legas, Rilwan Akiolu Majiyar mu, ta tattaro cewa, sarkin, wanda ya yaba wa Tinubu game da kokarinsa na gina Legas, ya kuma bayyana cewa ba za a iya kwace jihar a hannun APC ba. Har ila yau, sarki ya yaba da ayyukan gwamna Akinwunmi Ambode na jihar Legas. “Ba na ɓoye zuciyata, babu wanda zai iya kwace Legas a hannun APC. A tarayya kuma ya kamata mu hada karfin mu waje daya” , inji shi.

Jam’Iyyun APC Da PDP Sun Yi Na’am Da Tsayawa Takarar Shugaba Buhari A Zaben 2019 – Rochas Okorocha

Image
Yayin ganawa da kungiyar matasan dimokuradiya a ranar Talatar da ta gabata a fadar gwamnatin jihar dake birnin Owerri, Okorocha ya bayyana cewa, in banda biyu ko uku, dukkanin gwamnoni na jam’iyyu biyun suna goyon bayan sake tsayawa takara na shugaba Buhari a zaben 2019. A wata sanarwa ta Okorocha da sanadin sakataren gwamnatin jihar mai hurda da manema labarai, Sam Onwuemedo ya bayyana cewa, Ina da cikakken yakini akan shugaba Buhari kuma na zamtowar shi gwarzo wanda zai juyar da akalar shugabancin kasar nan, duba da tarihin da ta tara. “Babu mutum mafi dacewa da shugabancin Najeriya irin Buhari. Babu lallai a shekarar 2023 ko 2027 ya zamto mafi dacewa, amma a halin da Najeriya take ciki shine kan gaba wajen dacen shugabancin ta.” Rochas Okorocha tare da Shugaba Buhari “Yakar cin hanci da rashawa ba karamin aiki bane wanda sai irinsu Buhari ne kadai zasu jure. Tsare-tsaren sa ya sanadin kawo karshen ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas, wanda shi kan shi wata jarumta ce ta ...
Image
Najeriya C Gwamnatin Najeriya ta bukaci cibiyoyi masu zaman kansu dasu hada kai da jami’an gwamnati na kiwon lafiya domin yaki da zazzabin cizon sauro. Likitoci a Najeriya, sunce yanzu an daina amfani da tsofaffin magunguna irin su Chloroquine da Fansidar wajen maganin zazzabin cizon sauro domin sun daina tasiri. Yanzu dai an kawo sabuwar kwayar maganin yaki da maleriya ta ACT, wadda babban sinadarin cikinta shine Artemisinin, dake taimakawa wajen rabuwa da wannan cuta da sauro ke haddasawa. Jami’in yaki da Malaria na Najeriya, malam Abdu Muhammad, yace yara talatin (30) ke mutuwa a a cikin ko wani sa’a daya a Najeriya sanadiyar zazzabin cizon sauro. Hukumar yara ta Majalisar Dinkin Duniya, tace duk wuni malaria na kashe yara ‘yan kasa da shekara biyar su dubu biyu da dari uku a Najeriya, abinda yasa Najeriya, ta zama kasa ta biyu a yawan mutuwar yara ‘yan kasa da shekaru biyar a duniya. Jami’in yaki da zazzabin na hukumar lafiya ta duniya a Najeriya (WHO) Rex yace gara a dage ...

Gwamnatin Tarayya Bata Amince Da Saurin Binne ‘Yan Najeriya 26 Da Suka Mutu A Kasar Italiya Ba,

Gwamnatin tarayya ta bayyana matukar mamaki da kaduwa bisa saurin binne wasu ‘yan mata 26 ‘yan Najeriya da hukumomi suka yi a kasar Italiya bayan bayyana cewar sun mutu ne a tekun bahar maliya. Gwamnatin tarayya bata amince da saurin binne ‘yan Najeriya 26 da suka mutu a kasar Italiya ba Ofishin jakadancin kasar Italiya ya aike da takarda ga babban darekta a hukumar hana safara da fataucin mutane ta kasa, Julie Okah-Donli, cewar za a binne ‘yan Najeriyar ne ranar 26 ga watan Nuwamba a garin Salerno na kasar Italiya amma sai kawai hukumomi a kasar suka binne ‘yan matan ranar 17 ga watan Nuwamba Gwamnatin tarayya ta bayyana wa manema labarai cewar tuni ta aike da matsayar da ta dauka ga hukumar kasar Italiya ta ofishin jakadancin kasar dake Najeriya. A kwanakin baya ne rahotanni suka bayyana cewar wasu ‘yan mata 26 ‘yan Najeriya sun rasa ran su a hanyar su ta ketarawa zuwa kasar Italiya bayan da jirgi ya kife da su a gabar teku daf da wani garin kasar ta Italiya.

Shugaban Zimbabwe Mugabe Ya Ki Yayi Murabus Jiya Lahadi

Image
​ Robert Mugabe shugaban Zimbabwe yayinda yake yiwa al’ummar kasar jawabi jiya Lahadi ta kafar talibijan Yayinda jama’ar kasar ke kyautata zaton shugaban kasar Robert Mugabe zai yi murabus daga mukaminsa jiya Lahadi sai ga shi ya yi kememe har yana cewa shi ne zai jagoranci taron jam’iyyarsu watan gobe Dadadden Shugaban Zimbabwe Rober Mugabe na fuskantar tsigewa bayan da ya bayyana karara a wani jawabi ta kafar talabijin cewa ba fa zai sauka ba, Miliyoyin ‘yan kasar sun bude rediyonsu jiya Lahadi da fatan za su ji abin da zai sa su yi murnar kawo karshen abin da ya kasance tsawon shekaru 37 na mulkin kama karya da Mugabe ya yi. Sun yi matukar takaicin abin da ya faru, wasu ma har kuka su ka yi ta yi, bayan da su ka ji Mugabe ya ce shi ne ma zai jagoranci taron jam’iyyarsu ta ZANU-PF da za a yi watan gobe. Jam’iyyarsu mai mulkin kasar ta bashi wa’adin zuwa yammacin yau Litini ya yi murabus ya kuma nada mataimakin Shugaban kasa da ya kora Emmerson Mnangawa a matsayin ja...

Matsalar Hanya Tana jawowa Manoman Shinkafa cikas A Jihar Borno,

Image
Manoman shinkafa a Zarbamari yadda suke fama da rashin hanya, sai sun yi anfani da dabbobi su bi ta cikin ruwa Kauyan Zarbamari dake karamar hukumar Ciri cikin jihar Borno ya shahara da noman shinkafa inda mutane 5000 ne ke noman ta amma matsalar hanya na ci masu tuwo a kwarya kuma sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta taimaka. Mutanen Zabarmari sun kware a noman rani na shinkafa irin ta gida. Baicin noman shinkafar sukan sarafa ta da kansu. Rashin kyakyawar hanya da zata hadasu da Birnin Maiduguri, babban Birnin jihar na kawo masu cikas duk da cewa tazarar dake tsakanin Zarbamari da Maiduguri kilomita bakwai ne kawai. Alkalumma sun nuna cewa mutanen dake garin sun fi dubu arba’in kuma akasarinsu manoma shinkafa ne. Amma akwai kimanin mutane 5000 da suke noman shinkafa gadan gadan da kuma suke samar da shikafa fiye da ton miliyan hudu. Sai dai rashin hanya zuwa Maiduguri ya kawo masu cikas wajen hada hadar kasuwanci. Malam Hassan Muhammad shugaban kungiyar manoma shinkaf...

Jamiyya Mai Mulki Ta Kasar Zimbabwe Ta Sallami Shugaba Robert Mugabe

Image
​ ZIMBABWE ARMY TAKES CONTROL OF GOVERNMENT — Zimbabwean President Robert Mugabe (C) makes his first public appearance four days after the Zimbabwe National Army (ZNA) took over control of government in Harare, Zimbabwe, 17 November 2017. Jamiyya mai mulkin kasar Zimbabwe ta sallami shugaba Robert Mugabe daga shugabancin jamiyyar kana ta bukace shi da yayi murabus daga shugabancin kasar Shugabanin jamiyyar ZANU-PF na shugaba Robert Mugabe yau sun sallami Mugaben a matsayin shugaban jamiyyar kana sun nada tsohon mataimakin shugaban kasar Emerson Mnangagwa a matsayin sabon shugaban jamiyyar, idan dai ba a manta ba a cikin satin data gabata ne Mugabe ya kori mataimakin nasa wato Emerson. Haka kuma shugabannin jamiyyar sun kori matar Mugabe Grace a matsayin shugaban Mata na jamiyyar, harma daga cikin jamiyyar gaba daya. Yanzu dai idan Mugabe bai sauka daga kan shugaban cinkasar ba domin kashin kansa ba to abu na biyu da ka iya biyo bayya shine majilisar dokoin kasar ta tsig...

Assalamu alaikum

Image
Barka da wannan lokaci da fatan kowa yana cikin koshin lafiya, sunana Nura Muhammad Mai Apple Gusau.

Nigeria: An Tsaurara Tsaro A Zaben Jihar Anambra

Image
​ Ana gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya cikin tsauraron matakan tsaro. Babu wurin da aka samu rahoton tashin hankali, yayin da jami’an zabe suke ci gaba da aikin tantance masu kada kuri’a a safiyar Asabar. Jami’an tsaro sun ci gaba da sintiri a duk fadin jihar musamman a garin Onitsha, inda kungiyar da ke fafutikar ballewa daga Najeriya IPOB da kuma kungiyar MOSSOB suke da karfi. Jam’iyyu 37 ne za su fafata a wannan zabe mai cike da cece-ku-ce, ko da yake ‘yan takarar jam’iyyu biyar ne suka yi fice wato: Tony Nwoye na APC Gwamna Willie Obiano na APGA Oseloka Obaze na PDP Godwin Ezeemo PPD Osita Chidoka na UPP Wasu mazauna garin Akwa babban birnin jihar Anambra su sun ce shirye-shirye sun kammala ta fuskar gudanar da zaben da batun sha’anin tsaro da dai sauransu. Sai dai sun ce IPOB ta rika yada takarda da ke cewa “zabe ba zai gudana ba” . Kugiyar ta kuma nemi mutane akan su zauna a gida, kada su fita. Wakilin BBC ya ...

Tsagerun Neja-Delta A Jihar Ondo Sun Ajiye Makamai, Sun Rungumi Afuwar Da Gwamnati Tayi Musu

Image
Tsagerun Neja-Delta a Jihar Ondo sun tuba kuma sun ajiye makaman su. Hakan ya faru ne saboda sabon afuwa da bada tallafi da gwamnati tayi. Irin wannan afuwa dai ba sabon abu bane kuma irin wannan shirin yana bawa tsageran damar canja rayuwarsu ta hanyar koyan sana’a da kuma karatu wanda zai amfane su kuma ya amfani Jihar baki daya. Ga hotunan makaman da tsageran suka kawo a yayinda Shugabanin hukumar Soji da manyan Jami’an gwamnati a Jihar ke karban su. Hotuna: Tsagerun Neja-Delta a Jihar Ondo sun ajiye makamai, sun rungumi afuwar da gwamnati tayi musu.

Ana Wata Wa Wata: Jami’An ‘Yan Sanda Sun Warware Bama-Bamai 2 Yayin Da Ake Shirin Gudanar Da Zaben Jihar Anambra

Image
​ Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa, da misalin karfe 12:30 na ranar Jumma’ar da ta gabata, an tsinto wasu dasassun bama bamai guda biyu a daidai ofishin ‘yan sanda dake Arewacin jihar. Majiyar mu ta fahimci cewa, an samu nasarar jami’an ‘yan sanda da suka yi azamar kawar da wannan ibtila’i na tagwayen bama bamai, inda mataimakin sufeto janar na ‘yan sandan jihar Joshak Habila ya jagoranci lamarin. Wannan lamari ya tayar da hankula da dama sakamakon gabatowar zaben gwamna a jihar, wanda doriya akan wannan, zartacciyar kungiyar ta’adda ta IPOB ta sha alwashin tawartsa gudanarwar zaben jihar.

‘An Mayar Da Mu Saniyar Ware’ — Niger Delta

Image
​ Wasu Shugabannin a yankin Neja Delta na ci gaba da tofa albarkacin bakin su dangane da barazanar da wasu masu tada kayar baya a yankin suka yi cewa zasu koma farfasa bututan mai a yankin. Farfesa Akasoba Zainab Duke-Abiola, matar wani basarake ce a yankin, kuma shugabar wata kungiyar wanzar da zaman lafiya a Najeriya, ta shaida wa BBC cewa, duk da kundin tsarin mulkin kasa ya basu damar su yi bore, ai bai ba su damar su tayar da hankalin jama’a ba. Ta ce abin da ta ke gani ya harzuka masu tayar da bayan har suka yi wannan barazana shi ne, saboda ba a kula da su, an mayar da su saniyar ware tamkar baki a cikin kasarsu. Farfesar ta ce, duk wani tago mashi da ‘yan Najeriya ke samu, ba bu ‘yan yankin Neja Delta a ciki,don haka me ake so suyi? gwamnati ce yakamata ta dubi lamarinsu. Shugabar kungiyar ta ce, ba bu wani kwakkwaran shugabanci a yankin Neja Delta, shi ya sa ganin shugaban kasa ma su kai kokensu ke musu matukar wuya. Farfesa Akasoba, ta ce yakamata a hadu da ...

‘Kwalaben Codeine Miliyan Uku Ake Sha A Kano Da Jigawa A Kullum’

Image
​ Matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi ta zama ruwan dare game duniya, musamman a arewacin Najeriya. Abin da tada hankali shi ne yadda ‘yan mata suke shiga irin wannan mummunar dabi’a. Tun daga fatauci da sayarwa da kuma kwankwadar miyagun kwayoyin. Me yake sa su shiga harkar? Me zai ya sa mace wadda take rayuwar kyakkyawa ta fara tu’ammali da miyagun kwayoyi, wanda hakan yake mummar cutar da rayuwa. Na gana da wadansu ‘yan mata a birnin Kano wadanda suke tu’ammali da miyagun kwayoyi, wadanda suka guje wa gidajensu, suna yawo daga otel zuwa otel ko kuma dakunan samari. Har ila yau na tattauna da Mummy, daya daga cikin manyan dilolin miyagun kwayoyin mata . Ta shaida min cewa galibin masaya kwayoyin mata ne. Kamar yadda ta ce, galibin masu sayan kayan mayen matan aure wadanda suke fama da bakin cikin zamantakewar aure. Kuma suna shan kwayoyin ne saboda su dauke hankalinsu daga damuwar da suke ciki. Hakazalika na hadu da wata yarinya wadda ta ce min ta fara shan ...

An Tsinci Gawar Dan Jaridar Daya Bata A Anambara

Image
​ ‘Yan sanda sun tsinci gawar wani dan jarida ma’aikacin Anambara Broadcasting Service mai suna Ikechukwu Onubogu bayan kwana hudu da iyalan sa suka shigar da kara a wajen ‘yan sanda cewa ya bata basu gan shi ba. ‘Yan sandan Najeriya Har yanzu dai ba’a tantance menene ya janyo ajalin nasa ba. Matar sa ta ce suna gida sai aka kira shi a waya a ranar 12 Nuwamba da rana; bayan nan ya dauki kyamarar sa ya fita; daga nan bai sake dawowa ba. ‘Yan sanda sun tsinci gawar a Obosi, kusa da Onitsha. A yanzu haka sun mika da gawar zuwa Asibitin Koyarwa na Amaku, da ke Awka, Da aka nemi ji daga bakin shugaban ABS Uche Nworah, ya ce, “Mista Onubogu mutumin kirki ne kuma ba’a san shi da hayaniya ba. Babu yadda za’a yi mutum yai zaton wasu zasu yi masa haka. “Duk ma’aikacin ABS ya yi jimamin mutuwar nan saboda Onubogu na da hazaka wajen aiki. Ga shi da kurdakurda wajen iya nemo labarai. “Muna yi wa iyalin sa jaje, musamman matar sa da ta haihu a kwanannan.” Ya gama da cewa wannan...

Yanzu-Yanzu: Hukumar JAMB Ta Tsaida Ranar Da Za’A Rubuta Jarrabawar 2018

Image
​ A safiyar yau Laraba ne hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandiri JAMB ta bada sanarwan cewa zata gudanar da jarabawar shekarar 2018 ne a daga ranar 9 – 17 na Mayun 2018. Shugaban hukumar Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bada sanarwan a wani taron masu ruwa da tsaki a fanin ilimi. Yace an tsayar da ranakun jarabawar ne bayan anyi la’akari da ranakun da dalibai zasu rubuta wasu jarabawan. Ya kara da cewa hukumar zata gudanar da jarabawar gwaji daga 22 ga watan Janairu zuwa 27 na watan duk dai a shekarar 2018 din. Har ila yau, yace kudin rubuta jarabawar JAMB din yana nan kamar yadda aka sani N5000.

Yan kasuwa Sun Zubar Da Hawaye Yayin Da Gobara Ta Kama Shaguna A Birnin Akure

Image
​ A ranar Talatar da ta gabata ne ‘yan kasuwar suka rinka zubar da hawaye yayin da suke bayyana irin asarar da suka tafka sakamakon wannan gobara da afku da misalin karfe 2:00 na dare a babbar hanyar Roadblock dake daura da wurin sayar da abinci na Chicken Republic. ‘Yan kasuwa sun zubar da hawaye yayin da gobara ta kama shaguna a birnin Akure Labaran majiyar mu. ta ruwaito da sanadin jaridar Daily Trust cewa, wannan gobara ta afku ne sakamakon wata ‘yar matsala ta wutar lantarki, inda mazauna yankin suka yi iyaka bakin kokarin su na kashe wutar bayan ta debi awanni tana aika-aika a shagunan kafin zuwan ‘yan kwana-kwana. Dukiyoyi na tarin miliyoyi sun salwanta a cikin shagunan da wannan gobara ta lashe, inda ‘yan kasuwar suka bayyana cewa mafi akasarin hajojin su sababbi ne da suke shirin cin kasuwar bikin kirsimeti da kuma sabuwar shekara.

Taron Gangami: Yadda ‘Yan Takarar Shugabancin Jam’Iyya PDP Suka Sha Tambaya Yajen Gwamnoni 11

Image
​Wannan muhimmin taron dai kamar yadda majiyar mu tattaro na daya daga cikin shirye-shiryen jam’iyyar tare da dukkan masu ruwa da tsaki wajen ganin an samu kyakkyawan hadin kai musamman ma don ganin sun kwace mulki a zabe mai zuwa. Majiyar mu dai ta samu cewa wasu daga cikin mahalarta taron sun hada da shugaban riko na jam’iyyar Sanata Ahmad Makarfi, sai dukkan gwamnonin jam’iyyar in banda na jihar Ebonyi da mataimakin sa ya wakilce shi da kuma wasu daga cikin tsaffin gwamnonin jam’iyyar. Sauran mahalarta taron sun hada da Bode George, Uche Secondus, Tunde Adeniran, Jimi Agbaje, Taoheed Adedoja, Gbenga Daniel, Raymond Dokpesi da kuma Rashidi Ladoja. A karshen taron kuma an yanke shawarar cewa dukkan yan takarar zasu sa hannu a kan yarjejeriyar zaman lafiya.

Muna Kokarin Tura Malaman Makarantan Da Muka Sallama Wasu Wurare – Inji Gwamnan Kaduna ​

Image
​ Mun samu labari cewa Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai na shirin jefa Malaman Makarantar da ya sallama kwanan nan zuwa wasu fannin na dabam. Ku na da labari cewa Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya sallami Malaman makaranta sama da 20,000 kwanan nan bayan sun fadi jarrabawar ‘yan firamare. Sai dai Gwamnan yace yana duba inda zai jefa wadannan Malaman a Jihar. Gwamnan zai dauki wasu sababbin Malamai a Jihar kwanan nan. Gwamnan ya bayyana haka ne ta shafin sa na Tuwita a jiya bayan da wani Mutumi Bashir Muzakkar ya nemi ya ba Gwamnan shawarar yadda ya dace ayi da Malaman da aka kora. Gwamnan yayi na’am da wannan ya kuma nemi ya turo masa shawarar sa a sakon Email domin ya duba. Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa tun da su ka hau mulki su ke kokarin ganin yadda za ayi game da harkar ilmi a Jihar Kaduna. Gwamnan dai ya nemi duk wata mai shawara ya aiko masa ta akwatin kamar yadda ku ka ji. Da dama dai sun yi kira a nemawa Malaman wnai aikin.

Masu Neman Shugabancin PDP Zasu Rattaba Hannu A Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Ranar Talata – Inji Dokpesi

Image
​ Jigo a jam’iyyar adawa ta PDP, Cif Raymond Dokpesi kuma daya daga cikin ‘yan takarar neman shugabancin jam’iyyar, ya ce dukkanin masu neman takara su 8 za su rattaba hannu a yarjejeniyar zaman lafiya a matsayin wani ɓangare na samun nasara a babban taron da za a yi a watan Disamba. Dokpei, wanda ya kafa kamfanin Daar Communications, ya bayyana wannan a cikin wata hira da manema labarai bayan taro inda kungiyar gwamnonin PDP ta gana da dukan masu neman takara a Enugu, wanda aka kammala a safiyar yau Litinin. Kamar yadda majiyar mu, ke da labari , Dokpesi ya bayyana cewa duk masu neman takara sun amince da su shiga yarjejeniyar zaman lafiya a babban sakatariyar jam’iyyar, Wadata Plaza, wanda ke birnin Abuja a daidai karfe 4 na yamma. Ya ce ‘yan takara sun amince suyi aiki tare. Gwamnan jihar Ekiti kuma shugaban kungiyar gwamnonin PDP, Mista Ayodele Fayose ya bayyana cewa taron koli na kasa, wanda za a gudanar a ranar 9 ga watan Disamba, zai zama wata abin koyi ga sauran ...

An Bukaci A Nisanta Addini Daga Bakar Akidar Boko Haram

Image
​ Sakataren Kungiyar Kiristocin Najeriya Rabaran Musa Asake da Shugaban Kungiyar IZALA Shaikh Abdullahi Bala Lau a wurin kallon majigin da VOA ta shirya akan Boko Haram Yayinda ake ci gaba da nuna majigin Muryar Amurka akan Boko Haram mai taken Tattaki daga Bakar Akida shugabannin addini sun bukaci a nisanta addini da akidar Boko Haran tare da kiran hadin kai tsakanin Kirista da Muslmi a Najeriya A lokacinda ake nuna majigin Muryar Amurka kan yaki da bakar akidar Boko Haram malamai da kungiyoyin matasa sun nuna bukatar a bude sabon babi na nisanta addini daga muguwar masu kashe jama’a ba tare hakkin shari’a ba. Shugaban kungiyar IZALA Abdullahi Bala Lau da sakataren kungiyar Kiristoci ta Najeriya Rabaran Musa Asake sun nuna takaicin yadda ‘Yan Boko Haram suka cuci al’ummar da basu da laifin komi. Shaikh Abdullahi Bala Lau ya bukaci cewa a karantar da akida mai kyau. Yayi misali da irin gudummawar da Shaikh Jaafar Mahmud Adam ya bayar da har ya kai ga yi masa kisan gill...

Zaɓen 2019: Atiku Sai Ya Nemi Gafarar Obasanjo Muddin Yana Son Zama Shugaban Kasa A Najeriya

Image
​ Jonathan ya bayyana haka ne yayin wata hira da yayi da fitaccen dan jarida, shugaban kamfanin jaridar Ovation, Dele Momodu a gidansa dake babban birnin tarayya, Abuja. “Me kake gani game da yiwuwar Alhaji Atiku Abubakar na lashe zaben shugaban kasa?” sai Jonathan yace tabbas Atiku Abubakar dan kishin kasa ne, kamar yadda majiyar mu ta ruwaito. “Amma fa sai ya nemi Maigidanmu, Baba Obasanjo, shine Maigidan duk wasu Masu Gida, a yanzu mun gano babu wanda ya isa ya wulakanta Obasanjo ya kai labara. Obasanjo mutum ne wanda zai kullawa kuma ya warware, sa’annan ana ganin girmansa a ciki da wajen kasar nan.” Inji Jonathan. Sai dai da aka tambaye shi ko zai sake tsayawa takara a 2019, sai yace “A’a, ba zan sake tsayawa ba, baka da labarin jam’iyyar mu ta PDP ta mika takarar shugaban kasa ga Arewa ne?” Daga karshe ya tabbatar da cewa takarar shugaban kasa da gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose ya kaddamar zata fuskanci kalubale, saboda matakin da jam’iyyar mu ta dauka.

Malaman Polytechnic Din Najeriya Sun Fara Yajin Aiki Litinin

Image
​ Duk ilahirin malaman kwalejin kimiya da Fasaha, Polytechnic a Najeriya sun fara yajin aiki yau suna zargin gwamnatin tarayya da na jihohi da laifin nuna halin ko in kula bisa ga bukatunsu da suka hada da rashin biyansu albashi na watanni da dama A taron manema labarai da ya gudana a dakin taro na Tatari Ali Polytechnic dake Bauchi shugaban kungiyar malaman kwalajin Muhammad Bala Yakubu yace akwai abubuwa guda bakawi da suka tattauna a kai da hukumomin ilmi na jiha da na tarayya wadanda har yanzu ba’a cikasu ba. Muhammad Bala Yakubu ya ba al’umma hakuri da wannan yajin aikin da suka fara yana cewa ba sonsu ba ne amma kuma ya zama wajibi domin mahukunta da abun ya shafa su zabura su yi abun da ya kamata. Kafin su shiga yajin aikin wai sun bada wa’adi na kwana 21, da ya wuce suka kara kwana 10 amma gwamnati tayi kunnen lashi. Yace baicin rashin biyan su albashi na wata da watanni basu da kayan aiki a dakunan gwaje gwaje da bincike kana yawancin gine-ginesu suna neman rushe...

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’

Image
​ A Najeriya, yayin da ake ci gaba da cece-kuce game da dokar hana kiwo da ta soma aiki a jihar Benue da ke arewa ta tsakiyar kasar, ministan noma da raya karkara na kasar Audu Ogbeh, ya shaida wa BBC cewa saboda rikicin da ake yawan samu tsakanin manoma da makiyaya, dole ne a kintsa makiyayan wuri guda, sannan za’a samar da wurare na musamman domin shanu inda za’a basu ciyawa da ruwa mai kyau. Ministan ya ce, idan har aka yi hakan, to su kansu makiyayan ba za su so su yi yawo ba, kuma ko ba komai an kare su daga barazanar masu satar shanu. Dangane da batun kafa dokar hana kiwo a jihar Benue, ministan ya ce matsin lambar mutane ne ya tilasta wa gwamnan jihar kafa wannan doka saboda tashe-tashen hankulan da ake samu tsakanin manoma da makiyaya a jihar. Mr Audu Ogbeh, ya ce nan ba da jimawa ba za’a fara aiki a wuraren kiwo na musamman da aka kebe, na farko a jihar Kano, sai kuma na jihar Neja. Ya ce da sannu a hankali mutane za su fahimci cewa lallai ana bukatar naman shan...

Fadar Shugaban Kasa Ta Bayyana Abin Da Buhari Ya Tattauna Tare Da Shuagabannin Addinan Kirista Da Musulunci

Image
​ A ranar Juma’a ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya tabbatar wa shuwagabannin addinai da sauran ‘yan Najeriya cewan gwamnatin sa za ta magance mastalolin cin hanci da rashawa, almundahana, rashin adalci da rashin tsaro a sassan Kasan nan. Ya yi wannan jawabi ne yayin tarban wakilan al’ummar kirista da na musulmi, a lokuta mabambanta na ranar, karkashin jagorancin shuwagabannin kungiyoyin addinan na CAN da JNI. Buhari ya shaidawa wakilan CAN cewa ya bayar da umurnin a gabatar ma sa da sunayen shuwagabannin ma’aikatu da hukumomi domin bincike game da zargin daukan aiki ba bisa ka’ida ba. Buhari ya kuma ba su tabbacin kawo gyara cikin harkar Hukumar ‘yan sanda da ta Shari’a. Ya ce da su ne za a samu tsaro da adalci da nutsuwa. Ya kuma yi kira ga ga shuwagabannin addinan da a hada karfi da karfe wurin magance almundahana da cin hanci da rashawa. Don a cewar sa ga wakilan JNI, cin hanci da rashawa ya bi jinin ‘yan Najeriya, sai an yi taron dangi za a iya magance shi. Waki...

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Image
​ Kungiyar ta gindayawa shugaban kasa sharadi da cewar, in har yana son goyon bayan su a zaben 2019 to sai ya sauya kujerar da mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo yake kai a yanzu da wani dan kabilar su na yankin Kudu maso Gabashin kasar nan Majiyarmu  ta fahimci wannan sharadi ya zo ne bayan da shugaba Buhari ya yanke shawarar ziyartar jihohin Kudu maso gabashin kasar a makonnin da suka gabata. A wani rahoto da sanadin shugaban kungiyar Chilos Godsent da ya bayyana a birnin Owerri na jihar Imo, ya ce wannan ita kadai ce hanyar da jam’iyyar APC za ta samu goyon bayan su a zaben kasa na 2019. Godsent ya kara da cewa, jam’iyyar APC ta maishe da yankin na su saniyar ware wajen gudanar da shugabancin ta a kasar.

Tsagerancin Neja Delta: Sojin Ruwan Najeriya Sun Tanadi Jiragen Ruwa 20 Don Yin Sintiri A Jihar Delta

Image
​ Mukaddashin Kakakin rundunar sojin a babbar hedi kwatar su, Kaftin Suleman Dahun ne ya bayyana hakan a wani rahoton ranar Jumma’a ta yau a birnin tarayya. Jahun ya bayar da rahoton cewa, wannan kaddamar da jiragen ya na daya daga cikin manyan manufofi da dabarun na shugaban hafsin sojin ruwa Ibok Ete-Ike Ibas. Ya kuma ce za a kaddamar da jiragen dominn inganta ayyukan dake kan sojin. Ya ke cewa, wannan yunkuri zai kawar da laifukan; satar danyen man fetur, kafa matatun man fetur da ba bisa ka’ida ba da kuma sauran laifuffuka dake tayar da zaune tsaye a yankunan ruwa. A yayin haka dai, hukumar sojin ruwan ta mika godiyar ta kan irin goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen ingantawa kokarin da hukumar take yi.

RA'AYIN NURA MAI APPLE A KAN KORAR MALAMAI DA GWAMNAN JIHAR KADUNA, MALAM NASIR YAR RUFA'I YAKE SHIRIN YI!

Image
Assalamu Alaikum. Barka da wannan lokaci mai Albarka da fatan mai karatu yana Cikin koshin lafiya, Ko shakka babu, yunkurin da gwamnan jihar Kaduna yake shirin yi,  na korar wasu daga cikin masu Aikin malanta har kusan Dubu Ashirin da biyu(22,000)wani babban abin koma baya ne,  kuma da tir da Allah waddai ne. Shin meyasa gwamna Malam Nasir Yar Rufa'i.  Wannan aika-aikar.  Domin kuwa inada  matukar yakinin cewa a cikin wadan nan bayin Allah akwai masu mata sama daya, haka akwai masu 'ya 'ya samu da daya.  To ashe kuwa inhar haka ne!   Suna da wadanda suke ci a karkashin su, adadin lunkin balunka,  shin baya tunanen  iyalan  wadan nan bayin Allah zasu iya shiga cikin wani mawuyacin hali. Shawarar Nura mai Apple  a nan shine! Babbar shawara ta nan shine, duk Wanda ankace bai iya abu ba,  to meyake bukata`` babban abunda yake bukata a nan shine a jajirce wajin koyamasa abin har ya'iya kuma yasan me ake nufi da abun...

Abinka Da Tsohon Soja, Buhari Ya Tsaya Ki-Kam Tsawon Mintuna 69 A Wani Babban Taro

Image
​ Ko a jiya, yayin gabatar ma yan majalisun Najeriya kasafin kudin shekarar 2018, sama da awa guda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kwashe yana tsaye, yana zazzage musu jawabi. Shugaba Buhari ya fara jawabinsa ne tun daga karfe 2:22 na rana, zuwa karfe 3:31, a tsaye, inda jawabinsa nasa ya kunshi kalamai guda dubu shidda (6000) kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana. Majiyar mu.   ta ruwaito shugaban ya iso majalisar ne da misalin karfe 2:02, inda ya samu rakiyar mataimakin Kaakakin majalisa, Yusf Lasun, uban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, Sanata Kabiru Gaya da sauransu. Daga bangaren fadar shugaban kasa, Buhari ya samu rakiyar mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, hadimansa ta bangaren majalisun dokoki, Ita Enang da Abdulrahman Kawu Sumaila, ministan kasafin kudi da tsare tsare, Udo Udoma Udo da sauransu. Sauran da suka samu halartar taron sun hada da shugaban kungiyar gwamnoni, Abdul Aziz Yari, sh...

Fursunoni Mata Na Karuwa A Duniya

Image
Fursunoni Mata Na Karuwa A Duniya ​ Wani bincike da aka gudanar a kan yawan mata da ‘yammatan da ke zaman gidan yari a sassan duniya daban-daban, ya gano cewa adadin matan ya karu musamman a shekarun baya-bayan nan. Binciken ya kiyasta cewa yanzu haka akwai mata fiye da dubu dari bakwai da ke zaman gidan gidan kaso a duniya. A cewar wata cibiyar da ke bincike kan manyan laifuka da ke birnin London, adadin matan da ke zaman gidan kaso na karuwa a kowacce nahiya a cikin shekaru 17 da suka wuce, kuma an fi samun karuwar adadin fursunoni mata ne a kasashen Brazil da Indonesia da Phillipines da kuma Turkiya. Cibiyar ta ce, inda kuma ake da yawan fursunoni mata su ne Amurka da kuma China. An daure matar da ce mata na iya haihuwa babu aure ‘Mata ba za su yi daidai da maza ba nan da shekara 100’ A shekarar 2015, China ta samu karuwar fursunoni mata da yawa wadanda suka aikata laifukan da suka hadar sa sarafar miyagun kwayoyi da kuma cin hanci inji cibiyar. Hakan ya sa Chin...

Kasafin 2018: Buhari Na Shan Raddi Game Da Bawa Fanin Ilimi Kashi 7

Image
Kasafin 2018: Buhari Na Shan Raddi Game Da Bawa Fanin Ilimi Kashi 7 ​ Kungiyar Kare Hakkokin Musulmai (MURIC), ta yi Allah wadai da kashi 7 da a ka ba wa fanin ilimi a kasafin 2018 da Buhari ya gabatar ma Majalisa. Shugaban Kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, shi ne ya bayyana hakan a Ranar Laraba. Kungiyar ta yi nuni da cewan sakamakon halin ko-in-kula da wannan gwamnatin da gwamnatocin baya su ka yi ga harkar ilimi, ya sa harkar ta tabarbare. Ya isa misali yadda kashi 70 na dalibai sun kasa cin jarabawar shiga makarantun gaba da sakandare na 2017/2018. Haka dalibai ke fadi warwas ko wace shekara, in banda 2016 da a ka samu kashi 50 da su ka ci. Shi ma din ba wani abun alfahari bane, in ji kungiyar. Don kuwa Kungiyar Kula da Ilimi da Kimiyya da Al’adu na Majalisar Dinkin Duniya, (UNESCO), ta shawarci ba wa ilimi kashi 26 na kasafi. Ita kuwa Najeriya ko yaushe sai dai ta yi kunnen uwar shegu ga wannan shawara, ba a taba samun kaso mai tsoka ba, ballanta wanda ya kai kashi 2...