Ana Wata Wa Wata: Jami’An ‘Yan Sanda Sun Warware Bama-Bamai 2 Yayin Da Ake Shirin Gudanar Da Zaben Jihar Anambra






Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa, da misalin karfe 12:30 na ranar Jumma’ar da ta gabata, an tsinto wasu dasassun bama bamai guda biyu a daidai ofishin ‘yan sanda dake Arewacin jihar.

Majiyar mu ta fahimci cewa, an samu nasarar jami’an ‘yan sanda da suka yi azamar kawar da wannan ibtila’i na tagwayen bama bamai, inda mataimakin sufeto janar na ‘yan sandan jihar Joshak Habila ya jagoranci lamarin.

Wannan lamari ya tayar da hankula da dama sakamakon gabatowar zaben gwamna a jihar, wanda doriya akan wannan, zartacciyar kungiyar ta’adda ta IPOB ta sha alwashin tawartsa gudanarwar zaben jihar.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’