Skip to main content

An Bukaci A Nisanta Addini Daga Bakar Akidar Boko Haram






Sakataren Kungiyar Kiristocin Najeriya Rabaran Musa Asake da Shugaban Kungiyar IZALA Shaikh Abdullahi Bala Lau a wurin kallon majigin da VOA ta shirya akan Boko Haram

Yayinda ake ci gaba da nuna majigin Muryar Amurka akan Boko Haram mai taken Tattaki daga Bakar Akida shugabannin addini sun bukaci a nisanta addini da akidar Boko Haran tare da kiran hadin kai tsakanin Kirista da Muslmi a Najeriya

A lokacinda ake nuna majigin Muryar Amurka kan yaki da bakar akidar Boko Haram malamai da kungiyoyin matasa sun nuna bukatar a bude sabon babi na nisanta addini daga muguwar masu kashe jama’a ba tare hakkin shari’a ba.

Shugaban kungiyar IZALA Abdullahi Bala Lau da sakataren kungiyar Kiristoci ta Najeriya Rabaran Musa Asake sun nuna takaicin yadda ‘Yan Boko Haram suka cuci al’ummar da basu da laifin komi.

Shaikh Abdullahi Bala Lau ya bukaci cewa a karantar da akida mai kyau. Yayi misali da irin gudummawar da Shaikh Jaafar Mahmud Adam ya bayar da har ya kai ga yi masa kisan gilla. Y ace duk wani malami kuma da yayi yunkurin yin wa’azi akan akidar Boko Haram sai a kasheshi. Dalili ke nan malamai da yawa sun tsorata basa iya fitowa fili su kalubalanci kungiyar Boko Haram ba.

Shi ma Rabaran Musa Asake ya nuna damuwa da yadda ya ce gwamnati tayi sakaci da yaki da Boko Haram tare da cewa majigin na VOA ya fadakar dashi akan bukatar dake akwai Kiristoci da Musulmai su hada kai wajen wanzar da zaman lafiya. Yace da shugabannin addinan biyu sun zauna akan matsalar Boko Haram da sun yi maganin kungiyar. A cewarsa yanzu idan mutum yayi magana sai a bishi ana neman a kasheshi.

Kungiyar matasan Najeriya karkashin shugabancin Murtala Garba da wasu sun halarci taron.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Masana sun ce daga cikin abubuwan da suka sa dan Adam yin galaba a kan sauran halittu shi ne yadda yake iya hada kai. Don mutum shi kadai ba zai iya gwada karfi da zaki ko giwa ba. Amma idan ya hada karfi da sauran ‘yan uwansa babu kalubalen da ba za su iya tinkara ba. Hadin kai kuma ba ya tabbata sai da yarda, kuma yarda sai da mu’amala. Masu hikimar magana sun ce, Allah Ya halicce mu da kunne biyu, ido biyu amma sai ya yi mu da baki daya domin mu kalla, mu kuma saurara fiye da yadda muke magana.  Amma sai ya kasance cewa mun fi son yin magana fiye da saurare. Sau da yawa idan muna tattaunawa da wadansu ba ma mayar da hankali kan abin da ake fadi. Kawai jira muke mutum ya kai aya - idan ba mu katse shi ba kenan, domin mu fadi namu ra’ayin. Ga shi kuma ba mu son jin ra’ayoyin da suka sha bamban da namu. To ina za a samu fahimtar juna har a yi aiki tare?  Babu wanda rayuwarsa iri ɗaya da ta wani, kowa da irin  jarabawar shi,  kowa kuma da irin ta shi f...

A SAMARWA DA 'YAN GUDUN HIJIRA DA MASAUKAI!

A bisa ma'aunin Ilimi da hangen nesa, duk wanda ya baro garinsu, inda komai nasa a ce yake, kamar 'yan Uwansa da abokansa, mahaifansa, wadanda suke a raye da kuma wadanda Allah yayi rasuwa, kuma ya baro abincinsa wanda zaici, ya baro dabbobinsa wadanda ya dogara da su, Kacokan! ya fantsama yayi kaura zuwa wani waje, inda shima kansa bai san inda ya maida gaba ba, ina ganin wannan shine mafi munin tashin hankali da firgici da ɗimauta. A kullum a duk inda ka duba zakaga 'yan gudun Hijira ne birgik a saman tituna suna yawon barace-barace cikin kaskance da takaici, musamman yara 'yan Dagwai-dagwai wasunsu ma basu dade da fara iya tafiya ba, suna neman a taimake su, da abinda zasu ci, wasu daga cikinsu ko takalmin sakawa basu da haka nan suke yawo a Kasa cikin tagaiyara da nadama. Haka idon mukayi la'akari da yadda idon mutun ya saba da wajen zamansa akace ya tashi yabar wurin ba tare da kintsawa ba, yaya yake ji a cikin ransa? A 'yan baya-bayan nan shekaru biy...

ZAMU FADADA SHIRINMU NA YAZEED TRUST FUND MATERNITY CARE.......

Garkuwan matasan Gusau,Lamidon Tsafe wato Yazeed shehu Danfulani Mai Doya Gusau,ya jaddadar da ya zabi yaci gaba da zama hadimin al'umma arayuwarsa tare da bayyanar da kudurinsa akan baiwa lafiya fifiko musamman awannan lokaci da rayuwa ta soma tsada ga rayuwar bayin Allah sanadiyar cutar COVID-19. Lamidon Tsafe Yazeed Shehu Danfulani ya nuna tausayinsa ga yanda al'umma ke samun karancin shigar riba musamman Masu kananan sana'oin hannu,tare da tsaiko akan dakatuwar kasuwancinsu a wajen jahar zamfara(Yan fatauci). Hakan yasa Yazeed Danfulani yabada Umurnin fadada shirinsa na TAIMAKAWA MATA MASU DAUKE DA JUNA BIYU tare da fadakarwa akan hanyoyin kiyaye Lafiyar juna biyu da matakan dauka ayayin renon juna biyu,tare da bada Magunna Fisabilillah da fatar Allah saukar lafiya. Allah karfafa yasakama Yazeed da mafificin alhairi. YAZEED TRUST FUND. Rufai UB Gusau. 08106580400.