‘Kwalaben Codeine Miliyan Uku Ake Sha A Kano Da Jigawa A Kullum’
Matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi ta zama ruwan dare game duniya, musamman a arewacin Najeriya.
Abin da tada hankali shi ne yadda ‘yan mata suke shiga irin wannan mummunar dabi’a. Tun daga fatauci da sayarwa da kuma kwankwadar miyagun kwayoyin.
Me yake sa su shiga harkar?
Me zai ya sa mace wadda take rayuwar kyakkyawa ta fara tu’ammali da miyagun kwayoyi, wanda hakan yake mummar cutar da rayuwa.
Na gana da wadansu ‘yan mata a birnin Kano wadanda suke tu’ammali da miyagun kwayoyi, wadanda suka guje wa gidajensu, suna yawo daga otel zuwa otel ko kuma dakunan samari.
Har ila yau na tattauna da Mummy, daya daga cikin manyan dilolin miyagun kwayoyin mata . Ta shaida min cewa galibin masaya kwayoyin mata ne.
Kamar yadda ta ce, galibin masu sayan kayan mayen matan aure wadanda suke fama da bakin cikin zamantakewar aure.
Kuma suna shan kwayoyin ne saboda su dauke hankalinsu daga damuwar da suke ciki.
Hakazalika na hadu da wata yarinya wadda ta ce min ta fara shan miyagun kwayoyi ne bayan saurarinta ya yi watsi da ita.
Wata kuma ce min ta yi ta fara ne bayan mutuwar aurenta, lokacin da damuwa da kuma bakin ciki suka yi mata dabaibayi ne ta fara kwankwadar kwalaban Codeine.
Laifin wane ne? Na iyaye ne? Ko tsohon mijinta? Ta yaya har abin ya kai wannan matakin?
Comments
Post a Comment