‘An Mayar Da Mu Saniyar Ware’ — Niger Delta







Wasu Shugabannin a yankin Neja Delta na ci gaba da tofa albarkacin bakin su dangane da barazanar da wasu masu tada kayar baya a yankin suka yi cewa zasu koma farfasa bututan mai a yankin.

Farfesa Akasoba Zainab Duke-Abiola, matar wani basarake ce a yankin, kuma shugabar wata kungiyar wanzar da zaman lafiya a Najeriya, ta shaida wa BBC cewa, duk da kundin tsarin mulkin kasa ya basu damar su yi bore, ai bai ba su damar su tayar da hankalin jama’a ba.

Ta ce abin da ta ke gani ya harzuka masu tayar da bayan har suka yi wannan barazana shi ne, saboda ba a kula da su, an mayar da su saniyar ware tamkar baki a cikin kasarsu.

Farfesar ta ce, duk wani tago mashi da ‘yan Najeriya ke samu, ba bu ‘yan yankin Neja Delta a ciki,don haka me ake so suyi? gwamnati ce yakamata ta dubi lamarinsu.

Shugabar kungiyar ta ce, ba bu wani kwakkwaran shugabanci a yankin Neja Delta, shi ya sa ganin shugaban kasa ma su kai kokensu ke musu matukar wuya.

Farfesa Akasoba, ta ce yakamata a hadu da ainihin shugabannin da suka fito daga yankin don a lalubo bakin zaren matsalolin da yankin na Neja Delta ke fama da su, saboda gaskiya tura na kai wa bango.

Ta ce mutanen yankin ba su da isasshen abinci, don hatta masara idan aka dafa ba a cinta cikin dadi saboda fetur din da ake haka a yankin na su na bata musu abinci.

Shugabar kungiyar ta ce, baya ga rashin abinci, hatta ruwan sha mai tsafta ba su dashi a yankin, saboda hakar mai.

Farfesa Zainab ta ce, duk da wadannan matsaloli da yankin na su ke fuskanta, tana mai bawa masu fasa bututan mai shawara a kan su daina fasawa su kuma daina abinda suke yi saboda yin hakan ba a dauko hanyar zaman lafiya ba.

A bangaren gwamnatin kuma farfesar ta ce, yakamata gwamnati ta tattauna da mutanen da ya kamata, sannan ayi kokarin karbe sauran makaman da ke hannun masu tayar da kayar baya.

A kwanakin baya ne dai gwamnatin Najeriya ta ce a shirye take ta zauna da masu tayar da kayar bayan don jin korafin su game da matsalolin da suka addabi yankin.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’