Zimbabwe: Za’A Rantsar Da Emmerson Mnangagwa A Zaman Shugaban Kasa



Magoya bayan Emmerson
Mnangagwa suke rike da hotons a suna murna.

Kakakin majalisar dokokin kasar Jacob Metunda ne ya bada sanarwar haka Laraban nan.

Kakakin majalisar dokokin Zimbabwe Jacob Mudenda, ya ce za’a rantsar da Emmerson Mnangagwa, a zaman shugaban kasar ranar Jumma’a, biyo bayan murabus na Robert Mugabe, mutumin da ya juma yana mulkin kasar,al’amari da ya auku jiya talata.

Sanarwar da kakakin majalisar ya bayar a yau Laraba, tana zuwa ne a dai dai lokacinda Mnangagwa yake shirin komawas kasar. Haka kwatsam tsohon mataimakin shugaban ya gudu daga kasar a ranar shida ga watan nan, bayan da Mugabe ya kore shi daga kan mukaminsa.

Masu motoci sun yi ta busa kahon motocin su yayinda ‘yan kasar suke ta raye raye, da masu rangwada a Harare, babban birnin kasar don murnar murabsu din Mugabe, da ya bayyana jiya Talata, a cikin wasikar da kakakin majalisar Mudenda ya karanta a zauren majalisar.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’