Najeriya Ce Kan Gaba Wajen Samar Da Iri Na Noma A Yankin Afirka Ta Yamma – NASC



Shugaban cibiyar samar da iri na noma ta NASC (National Agricultural Seeds Council), Mista Philip O. Ojo, ya bayyana cewa, kasar Najeriya ce ke samar da kashi 75 na iri na noma da ake amfani da shi a gaba daya yankin Afirka ta Yamma, wanda hakan ya maishe da kasar kan gaba wajen samar da iri na noma a yankin.

Mista Philip ya bayyana hakan ne yayin da ya jagoranci tawagar cibiyar da ta ziyarci gwamnan jihar Jigawa Alhaji Badaru Abubakar, a ranar Litinin din da ta gabata.
Shugaban cibiyar ya bayar da jawabi da cewar, “kasar Najeriya ce ka samar da kaso 75 na irin shuka da ake amfani da shi a yankin Afirka ta Yamma, wanda hakan ya maishe da ita kan gaba wajen fitar da iri zuwa kasashen ketare dake nahiyyar.

Najeriya ce kan gaba wajen samar da iri na noma a yankin Afirka ta Yamma – NASC
“Wannan shine bigire da kasar ta yi fintikau, amma muna bukatar ta kara hobbasa yinkurin ta. Sai dai irin taimako da gudunmawa da wasu jihohin kasar suke bayar wa abin yabawa ne, kuma muna kyautata zaton wannan jihohi za su ci ribar gudunmawar da suke bayar wa.”

Mista Ojo ya kara da cewa, kamfanin iri da aka assasa kafa shi a jihar Jigawa alamu ne samar da cigaba domin inganta harkokin noma da gwamnatin jihar take yi.

A nasa jawabin gwamna Badaru ya bayyana cewa, samuwar iri managarta zai taimakawa jihar sa wajen inganta harkokin noma a dukkan wani sashe na ta, ya kuma hanya mafificiya wajen samun albarkar noma tana farawa ne da managartattun iri na shuka.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’