Kimanin Mutane 40,000 Neke Neman Aikin Malanta A Jihar Kaduna



A jiya Alhamis ne Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa kimanin mutane 40,000 suka mika takardun su ne neman aikin malanta a makarantun gwamnati da ke Jihar.

Gwamnan ya fadi wannan maganan ne kwanaki kadan bayan ya bayyana cewa gwamnatin sa zata sallami malamai makarantun firmare guda 21,780 wanda suka fadi jarabawar cacanta aiki da gwamnatin Jihar ta gudanar.

Kimanin mutane 40,000 ne ke neman aikin malanta a Jihar Kaduna
Hakan ne yasa gwamnatin Jihar tace zata maye gurbin malaman da zata sallama duk da cewa hakan bai yiwa mutane da yawa dadi ba har ma da kungiyar kwadigo na Jihar wanda ta jagoranci zanga-zangar lumana na nuna kin amincewa da sallamar malaman da gwamnatin Jihar ke niyyar yi.

Wata sanarwa da ta fito daga mai baiwa gwamnan Jihar Kaduna shawara kan kafafen yada labarai, Samuel Aruwan tace gwamnan ya bayyana adaddin masu neman aikin ne yayinda yake ganawa da ‘Yan Majalisar Tarayyah a Abuja a ranar Laraba.

Sanarwan ta cigaba da cewa El-Rufai ya roki ‘Yan Majalisar su taimaka su ceto al’ummar da zasu zo nan gaba ta hanyar basu ingantacen ilimi. Ya kuma kara da cewa duk wanda sukayi nasarar cin jarabawar da gwamnatin zatayi zasu samun horo na musamman kafin a tura su makarantun domin su fara koyarwa.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’