Skip to main content

A CIGABA DA TARON WAYAR DA KAN AL'UMMA DA KUNGIYAR MATASAN ZMF TA TSAKIYA KE GUDANARWA A SASSA DABAN DABAN NA YANKIN ZMF TA TSAKIYA


____________________________________

Kungiyar ta gana da alummar yankin mayanchi dake karamar mulki ta maru, Wanda taron ya gudana a fadar  uban kasar mayanchi .

Shugaban kungiyar Rufai bala ub ya bayyana Masu ayukkan kungiyar tareda bayyana Masu cewa Yana daga cikin manufofin wannan kungiyar Samar da shugabanci na gari.

A nashi jawabin comrade Nura bello Dan kishin kasa ya bayyana cewa matasa sune wadanda ke taimakawa wajen kawo cigaba Mai dorewa.

Darektan walwala da jin dadi ya bayyana cewa yanzu lokaci Yayi da yakamata abaiwa zamfara ta tsakiya damar rike kujerar gwamna laakari da yadda wannan yankin ya jajirce wajen taimakawa sauran yankuna, kuma ya zayyano dukkanin Masu neman kujerar gwamna daga wannan yanki.

Wani  daga cikin mahalarta taron ya nemi kungiyar matasan zamfara ta tsakiya akan tayi Kira ga hukumar INEC akan ta Kara fadada wuraren karbar Katin zabe, Sakataren uban kasar mayanchi Yayi tambaya akan yadda ake shiga wannan kungiyar.

Shi kuma wani Yayi Kira ga shuwagabannin kungiyar akan su taimaka wajen bayyana ma Masu rike da madafun iko akan matsalolin su, Kama daga hanyar su wadda ba tafi tsawon kilomita daya ba, sai bukatar bore hole da kuma gyaran masallacin jumaa dake ardo,  da kuma gyaran dakunan kwana na makarantar almajirai Mai sama da dalibbai dubu biyu,sai bukatar su ta fadada makabartar mayanchi da kuma bukatar wajen ba haya na almajirai sama da 2000.

wani abin mamaki shine wani gari Mai suna garagin Gobirawa, mazauna garin sun tabbatar muna cewa basu taba amfana da komai ba tun daga  1999 Har zuwa yanzu.

Da yake maida jawabi Sakataren kungiyar Ya amsa Masu da cewa inshaallahu zasu Mika dukkanin kokensu a wuraren da suka dace .
 
Daga karshe uban kasar Ya nuna farin cikin sa akan wannan taro tareda nasiha ga 'ya'yan wannan kungiyar akan su cigaba da zama tsinstiya madaurin ki daya Wanda da  hakan ne za'a samu dukkanin abinda ake nema.

VIA ANNUR AHMED MAGAZU P,R,O,2 MATASAN ZMF TA TSAKIYA

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Masana sun ce daga cikin abubuwan da suka sa dan Adam yin galaba a kan sauran halittu shi ne yadda yake iya hada kai. Don mutum shi kadai ba zai iya gwada karfi da zaki ko giwa ba. Amma idan ya hada karfi da sauran ‘yan uwansa babu kalubalen da ba za su iya tinkara ba. Hadin kai kuma ba ya tabbata sai da yarda, kuma yarda sai da mu’amala. Masu hikimar magana sun ce, Allah Ya halicce mu da kunne biyu, ido biyu amma sai ya yi mu da baki daya domin mu kalla, mu kuma saurara fiye da yadda muke magana.  Amma sai ya kasance cewa mun fi son yin magana fiye da saurare. Sau da yawa idan muna tattaunawa da wadansu ba ma mayar da hankali kan abin da ake fadi. Kawai jira muke mutum ya kai aya - idan ba mu katse shi ba kenan, domin mu fadi namu ra’ayin. Ga shi kuma ba mu son jin ra’ayoyin da suka sha bamban da namu. To ina za a samu fahimtar juna har a yi aiki tare?  Babu wanda rayuwarsa iri ɗaya da ta wani, kowa da irin  jarabawar shi,  kowa kuma da irin ta shi f...

LABOUR ROOM BLOBAL INITIATIVE KIRA NA MUSAMMAN ZUWA GA MATASA DA 'YAN SIYASA

Duk tarin dukiyarka, ko girman mulkinka ko zamanka basarake, ba zaka taɓa jin daɗin abinda kake taƙama da shi ba, matuƙar al`ummar da kake rayuwa a cikinta ba su zaune lafiya ko da kai ka tsira, kuwa. Shi dama talaka juji ne, duk wani tarin dattin tashin hankali, akansa yake ƙarewa. Da shi ake amfani wajen tashe-tashen hankula, shi ke kisa kuma shi ake kashewa kuma duk masifar da kan biyo baya a kansa ne take sauka. In ko haka ne, haƙiƙa da sake! kenan kowa na matuƙar kaunar zaman lafiya a cikin al'umma, domin sai da zaman lafiya ɗin ne, kowa zai iya morewa, har ya iya rayuwarsa ba tare da shiga tasko ba. A kan haka ne! Ƙungiyar Labour Room Global Initiative haɗin gwiwa da Ƙungiyoyin Jihar Zamfara ke amfani da wannan damar wajan kira ga dukkanin 'yan Siyasa, da ayi siyasa ba tare da gaba ba. Domin in dai har za'a iya zubar da jini a kashe rai a zaɓen fitar da gwani kurrum na jam'iyya ɗaya, to ina ga zaɓen gama-gari da ke tafe? Don haka muna amfani da wannan ...

A SAMARWA DA 'YAN GUDUN HIJIRA DA MASAUKAI!

A bisa ma'aunin Ilimi da hangen nesa, duk wanda ya baro garinsu, inda komai nasa a ce yake, kamar 'yan Uwansa da abokansa, mahaifansa, wadanda suke a raye da kuma wadanda Allah yayi rasuwa, kuma ya baro abincinsa wanda zaici, ya baro dabbobinsa wadanda ya dogara da su, Kacokan! ya fantsama yayi kaura zuwa wani waje, inda shima kansa bai san inda ya maida gaba ba, ina ganin wannan shine mafi munin tashin hankali da firgici da ɗimauta. A kullum a duk inda ka duba zakaga 'yan gudun Hijira ne birgik a saman tituna suna yawon barace-barace cikin kaskance da takaici, musamman yara 'yan Dagwai-dagwai wasunsu ma basu dade da fara iya tafiya ba, suna neman a taimake su, da abinda zasu ci, wasu daga cikinsu ko takalmin sakawa basu da haka nan suke yawo a Kasa cikin tagaiyara da nadama. Haka idon mukayi la'akari da yadda idon mutun ya saba da wajen zamansa akace ya tashi yabar wurin ba tare da kintsawa ba, yaya yake ji a cikin ransa? A 'yan baya-bayan nan shekaru biy...