Taron Gangami: Yadda ‘Yan Takarar Shugabancin Jam’Iyya PDP Suka Sha Tambaya Yajen Gwamnoni 11




​Wannan muhimmin taron dai kamar yadda majiyar mu tattaro na daya daga cikin shirye-shiryen jam’iyyar tare da dukkan masu ruwa da tsaki wajen ganin an samu kyakkyawan hadin kai musamman ma don ganin sun kwace mulki a zabe mai zuwa.

Majiyar mu dai ta samu cewa wasu daga cikin mahalarta taron sun hada da shugaban riko na jam’iyyar Sanata Ahmad Makarfi, sai dukkan gwamnonin jam’iyyar in banda na jihar Ebonyi da mataimakin sa ya wakilce shi da kuma wasu daga cikin tsaffin gwamnonin jam’iyyar.

Sauran mahalarta taron sun hada da Bode George, Uche Secondus, Tunde Adeniran, Jimi Agbaje, Taoheed Adedoja, Gbenga Daniel, Raymond Dokpesi da kuma Rashidi Ladoja.

A karshen taron kuma an yanke shawarar cewa dukkan yan takarar zasu sa hannu a kan yarjejeriyar zaman lafiya.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’