Zaɓen 2019: Atiku Sai Ya Nemi Gafarar Obasanjo Muddin Yana Son Zama Shugaban Kasa A Najeriya
Jonathan ya bayyana haka ne yayin wata hira da yayi da fitaccen dan jarida, shugaban kamfanin jaridar Ovation, Dele Momodu a gidansa dake babban birnin tarayya, Abuja.
“Me kake gani game da yiwuwar Alhaji Atiku Abubakar na lashe zaben shugaban kasa?” sai Jonathan yace tabbas Atiku Abubakar dan kishin kasa ne, kamar yadda majiyar mu ta ruwaito.
“Amma fa sai ya nemi Maigidanmu, Baba Obasanjo, shine Maigidan duk wasu Masu Gida, a yanzu mun gano babu wanda ya isa ya wulakanta Obasanjo ya kai labara. Obasanjo mutum ne wanda zai kullawa kuma ya warware, sa’annan ana ganin girmansa a ciki da wajen kasar nan.” Inji Jonathan.
Sai dai da aka tambaye shi ko zai sake tsayawa takara a 2019, sai yace “A’a, ba zan sake tsayawa ba, baka da labarin jam’iyyar mu ta PDP ta mika takarar shugaban kasa ga Arewa ne?”
Daga karshe ya tabbatar da cewa takarar shugaban kasa da gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose ya kaddamar zata fuskanci kalubale, saboda matakin da jam’iyyar mu ta dauka.
Comments
Post a Comment