Dalilin Da Yasa Har Yanzu Ana Damawa Da Tinubu A Siyasar Najeriya – Inji Sarkin Legas



Oba na Legas, Rilwan Akiolu ya bayyana dalilin da yasa jigon jam’iyya mai mulki ta APC, Bola Tinubu, har yanzu yana da matsayi a harkokin siyasa a Najeriya.

Sarkin ya ce takunsa ya sanya shi tsawon lokaci a siyasar Najeriya Najeriya.
Da yake jawabi a Ibadan, babban birnin jihar Oyo a ranar Talata, 21 ga watan Nuwamba, Akiolu ya ce,
“Jarumtakar Tinubu ya sanya shi a matsayin da yake a yau a lokacin da babban jam’iyyar adawa ta PDP ta matsa wa yankin kudu maso yammacin kasar lamba”.

Oba na Legas, Rilwan Akiolu
Majiyar mu, ta tattaro cewa, sarkin, wanda ya yaba wa Tinubu game da kokarinsa na gina Legas, ya kuma bayyana cewa ba za a iya kwace jihar a hannun APC ba.

Har ila yau, sarki ya yaba da ayyukan gwamna Akinwunmi Ambode na jihar Legas.

“Ba na ɓoye zuciyata, babu wanda zai iya kwace Legas a hannun APC. A tarayya kuma ya kamata mu hada karfin mu waje daya” , inji shi.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’