Matsalar Hanya Tana jawowa Manoman Shinkafa cikas A Jihar Borno,
Manoman shinkafa a Zarbamari yadda suke fama da rashin hanya, sai sun yi anfani da dabbobi su bi ta cikin ruwa
Kauyan Zarbamari dake karamar hukumar Ciri cikin jihar Borno ya shahara da noman shinkafa inda mutane 5000 ne ke noman ta amma matsalar hanya na ci masu tuwo a kwarya kuma sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta taimaka.
Mutanen Zabarmari sun kware a noman rani na shinkafa irin ta gida. Baicin noman shinkafar sukan sarafa ta da kansu.
Rashin kyakyawar hanya da zata hadasu da Birnin Maiduguri, babban Birnin jihar na kawo masu cikas duk da cewa tazarar dake tsakanin Zarbamari da Maiduguri kilomita bakwai ne kawai.
Alkalumma sun nuna cewa mutanen dake garin sun fi dubu arba’in kuma akasarinsu manoma shinkafa ne. Amma akwai kimanin mutane 5000 da suke noman shinkafa gadan gadan da kuma suke samar da shikafa fiye da ton miliyan hudu. Sai dai rashin hanya zuwa Maiduguri ya kawo masu cikas wajen hada hadar kasuwanci.
Malam Hassan Muhammad shugaban kungiyar manoma shinkafa a garin Zarbamarin yace matsalar hanyar da bata wuce kilomita bakwai ba yake ci masu tuwo a kwarya. Ya yi ga kira shugaban kasa Muhammad Buhari da ya taimaka masu da hanyar.
Comments
Post a Comment