Zaben 2019: Gwamnatin Buhari Tana Barazana Ga Hadin Kan Kasa – Inji Atiku



Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a matsayin babban barazana ga hadin kan kasa, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito. Majiyar mu ta tattara cewa Atiku ya rubuta wasika zuwa ga jam’iyyar APC, inda yake sanar da su shawararsa na ficewa daga jam’iyyar.

Ko da yake ya rubuta wannan wasiƙar ne a ranar 18 ga Oktoba, 2017, amma shugaban jam’iyya mai mulki ta APC a ranar Juma’a ya karyata karbar wannan sanarwa daga tsohon mataimakin shugaban.

A cikin wasikar, Atiku ya ce shawar ficewa daga jam’iyyar bai kasance game da shi ba, amma game da makomar kasar Najeriya.

“Na gagara fahimtar rashin aikin wannan gwamnatin jam’iyya mai mulki, musamman ma game da yadda al’amuran mutanen mu ke ta barbarewa ta hanyar kabilanci da addini wanda ke barazana ga hadin kanmu fiye da kowane lokaci a cikin ‘yan kwanan nan da kuma kalubale da al’ummar kasar ke fuskanta sakamakon durkushewar tattalin arziki”, in ji shi.

A cikin wasikar wanda Usman Muazu ya amince da shi, wanda kuma majiyar NAIJ.com ta samu, Wazirin Adamawa ya ce; “Ina so in sanar da ku game da shawarar yin murabus daga jam’iyyar APC a wannan rukunin wanda kuma za ta fara daga ranar da wannan wasika ta fito”.

“Na yi murabus daga wannan jam’iyyar da muka kafa kuma muka yi tsayin daka tare da ‘yan’uwanmu’ na siyasa a duk faɗin ƙasar, don mu sanya gwamnati. Ina fata cewa a wancan lokacin gwamnatin APC za ta inganta rayuwar jama’armu da ci gaban Najeriya a matsayin al’umma guda ɗaya. Amma wannan buri ta riga ta rushe”.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’