Gwamnatin Tarayya Bata Amince Da Saurin Binne ‘Yan Najeriya 26 Da Suka Mutu A Kasar Italiya Ba,
Gwamnatin tarayya ta bayyana matukar mamaki da kaduwa bisa saurin binne wasu ‘yan mata 26 ‘yan Najeriya da hukumomi suka yi a kasar Italiya bayan bayyana cewar sun mutu ne a tekun bahar maliya.
Gwamnatin tarayya bata amince da saurin binne ‘yan Najeriya 26 da suka mutu a kasar Italiya ba
Ofishin jakadancin kasar Italiya ya aike da takarda ga babban darekta a hukumar hana safara da fataucin mutane ta kasa,
Julie Okah-Donli, cewar za a binne ‘yan Najeriyar ne ranar 26 ga watan Nuwamba a garin Salerno na kasar Italiya amma sai kawai hukumomi a kasar suka binne ‘yan matan ranar 17 ga watan Nuwamba
Gwamnatin tarayya ta bayyana wa manema labarai cewar tuni ta aike da matsayar da ta dauka ga hukumar kasar Italiya ta ofishin jakadancin kasar dake Najeriya.
A kwanakin baya ne rahotanni suka bayyana cewar wasu ‘yan mata 26 ‘yan Najeriya sun rasa ran su a hanyar su ta ketarawa zuwa kasar Italiya bayan da jirgi ya kife da su a gabar teku daf da wani garin kasar ta Italiya.
Comments
Post a Comment