Tsagerancin Neja Delta: Sojin Ruwan Najeriya Sun Tanadi Jiragen Ruwa 20 Don Yin Sintiri A Jihar Delta
Mukaddashin Kakakin rundunar sojin a babbar hedi kwatar su, Kaftin Suleman Dahun ne ya bayyana hakan a wani rahoton ranar Jumma’a ta yau a birnin tarayya.
Jahun ya bayar da rahoton cewa, wannan kaddamar da jiragen ya na daya daga cikin manyan manufofi da dabarun na shugaban hafsin sojin ruwa Ibok Ete-Ike Ibas. Ya kuma ce za a kaddamar da jiragen dominn inganta ayyukan dake kan sojin.
Ya ke cewa, wannan yunkuri zai kawar da laifukan; satar danyen man fetur, kafa matatun man fetur da ba bisa ka’ida ba da kuma sauran laifuffuka dake tayar da zaune tsaye a yankunan ruwa.
A yayin haka dai, hukumar sojin ruwan ta mika godiyar ta kan irin goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen ingantawa kokarin da hukumar take yi.
Comments
Post a Comment