Abinka Da Tsohon Soja, Buhari Ya Tsaya Ki-Kam Tsawon Mintuna 69 A Wani Babban Taro







Ko a jiya, yayin gabatar ma yan majalisun Najeriya kasafin kudin shekarar 2018, sama da awa guda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kwashe yana tsaye, yana zazzage musu jawabi.

Shugaba Buhari ya fara jawabinsa ne tun daga karfe 2:22 na rana, zuwa karfe 3:31, a tsaye, inda jawabinsa nasa ya kunshi kalamai guda dubu shidda (6000) kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana.

Majiyar mu.   ta ruwaito shugaban ya iso majalisar ne da misalin karfe 2:02, inda ya samu rakiyar mataimakin Kaakakin majalisa, Yusf Lasun, uban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, Sanata Kabiru Gaya da sauransu.

Daga bangaren fadar shugaban kasa, Buhari ya samu rakiyar mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, hadimansa ta bangaren majalisun dokoki, Ita Enang da Abdulrahman Kawu Sumaila, ministan kasafin kudi da tsare tsare, Udo Udoma Udo da sauransu.

Sauran da suka samu halartar taron sun hada da shugaban kungiyar gwamnoni, Abdul Aziz Yari, shugaban jam’iyyar APC, John Oyegun, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari, sakataren gwamnati Boss Mustapha da kuma gwamnan bankin Najeriya, Godwin Emefiele.

Bayan kammala taron, sai yan majalisu da dama suka dinga rige rigen zuwa wajen shugaban kasa don gaisawa da shi, da Farfesa Yemi Osinbajo.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’