Buhari Ya Biya Kudin Makaranta Miliyan 164.8 Na ‘Yan Matan Chibok 106



Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya amince da biyan kuɗin dalibai na jami’a na ‘yan matan Chibok 106, fadar shugaban kasa a ranar Lahadi 26 ga watan Nuwamba ta sanar da hakan.
Mataimakin shugaban kasa a kan shafukan yanar gizo Lauretta Onochie ta tabbatar da hakan a shafinta ta Twitter a ranar Lahadi.

Ta ce ‘yan matan suna karatu ne a jami’ar Amurka ta Najeriya wanda ke garin Yola, jihar Adamawa, wanda tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya kafa.

Majiyar mu  ruwaito kwanan nan cewa iyayen sauran ‘yan makaranta na Chibok sun nuna bakin ciki ga shugaba Buhari game da makomar’ ya’yansu wadanda har yanzu suna hannun Boko Haram.

Iyaye, a cikin wata wasika da suka rubuta wa shugaba Buhari, sun bayyana cewa kimanin iyaye 20 daga cikinsu sun mutu yayin da suke jiran dawowar ‘ya’yansu.

Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin cewa, sauran ‘yan matan za su samu ‘yanci bayan masu tayar da kayar baya sun saki ‘yan mata 82 bayan musanya da wasu mayakan Boko Haram.

Bayan watanni 5, kungiyar ta sake sakin wasu ‘yan matan Chibok 21.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’