Wasu Manyan ‘Yan Siyasar Jihar Adamawa Su Biyu Sunyi Sa-in-sa Akan Kai Kayan Agaji
Lamarin dake kama da wasan kwaikwayo ya faru ne a babban filin jirgin sama na kasa da kasa dake Yola babban birnin jihar Adamawa, a lokacin da tawagar hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA ke shirin kai kayayyakin tallafi ga al’ummar Madagali, da rikicin Boko Haram ya shafa.
Bayanai na nuna cewa dan majalisar wakilai dake wakiltar al’ummomin yankin Michika da Madagali, Adamu Kamale ya nemi ya bi jirgin tawagar hukumar bada agajin NEMA mai saukar ungulu, to amma sai dan majalisar dattawa mai wakiltar Adamawa ta tsakiya Senata Abdul’Aziz Nyako, wanda ke zama shugaban kwamitin aiki da cikawa na majalisar kuma mai sa ido kan harkokin hukumar NEMA, ya ce dan majalisar wakilan ya sauka saboda babu sunansa a jerin wadanda zasu kai kayayyakin tallafin, batun da ya harzuka dan majalisar.
A wata takardar koke da ya rabawa manema labarai a Yola, dan majalisar ya zargi Sanata Abdul’Aziz Nyako da cin zarafinsa, da kuma hana shi sa ido game da kayayyakin da za a kai mazabarsa, abin da ya ce ba za ta sabu ba.
Sai dai Sanata Abdul’Aziz Nyako, ya musanta zargin, inda yace dan majalisar Adamu Kamale gayyar sodi ne da yaso ya hallaka kansa.
Bashir Idris Garga shine babban jami’in hukumar ta NEMA mai kula da jihohin arewa maso gabas, ya bayyana cewa babu sunan sanata Adamu Kamale a cikin jerin sunayen tawagar da za ta kai kayayyakin saboda bai bada sunansa ko na wakilinsa akan kari ba.
Comments
Post a Comment