Shugaban Zimbabwe Mugabe Ya Ki Yayi Murabus Jiya Lahadi







Robert Mugabe shugaban Zimbabwe yayinda yake yiwa al’ummar kasar jawabi jiya Lahadi ta kafar talibijan

Yayinda jama’ar kasar ke kyautata zaton shugaban kasar Robert Mugabe zai yi murabus daga mukaminsa jiya Lahadi sai ga shi ya yi kememe har yana cewa shi ne zai jagoranci taron jam’iyyarsu watan gobe

Dadadden Shugaban Zimbabwe Rober Mugabe na fuskantar tsigewa bayan da ya bayyana karara a wani jawabi ta kafar talabijin cewa ba fa zai sauka ba,

Miliyoyin ‘yan kasar sun bude rediyonsu jiya Lahadi da fatan za su ji abin da zai sa su yi murnar kawo karshen abin da ya kasance tsawon shekaru 37 na mulkin kama karya da Mugabe ya yi.

Sun yi matukar takaicin abin da ya faru, wasu ma har kuka su ka yi ta yi, bayan da su ka ji Mugabe ya ce shi ne ma zai jagoranci taron jam’iyyarsu ta ZANU-PF da za a yi watan gobe.

Jam’iyyarsu mai mulkin kasar ta bashi wa’adin zuwa yammacin yau Litini ya yi murabus ya kuma nada mataimakin Shugaban kasa da ya kora Emmerson Mnangawa a matsayin jagoran jam’iyyar.

Da babban kwamitin jam’iyyar ke daukar matsayi ya ce Chinamasa ya sauke Shugaban kasa daga manyan matsayi biyu na ZANU-PF:

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’