Gusau: Zamfara Ta Sami Sabuwar Kwamishinan ‘Yan Sanda
Sabon kwamishinan ‘yan sanda na jihar Zamfara, Mista Kenneth Ebrimson ya fara aiki.
Ebrimson, ya kasance daga sashin ayyuka na musamman a hedkwatar hukumar ‘yan sanda kuma ya maye gurbin tsohon kwamishina, Alhaji Shaba Alkali wanda aka sake dawo da shi a hedkwatar da ke birnin Abuja.
Sanarwar da jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar Zamfara, DSP Muhammad Shehu, ya bayar a ranar Juma’a, 24 ga watan Nuwamba, ta nuna cewa sabon kwamishinan ‘yan sandan ya ziyarci wuraren da ake rikici nan da nan don tsara yadda za a magance matsalolin yankin.
Hukumar ‘yan sanda
Ya ce, “Mun ziyarci yankin karamar hukumar Shinkafi daya daga cikin kananan hukumomin da ‘yan bindigar da ba a sani ba, suka kai hari a makon jiya”.
Ya ce sabon kwamishinan ya yi ziyarar ta’aziyya zuwa ga sarkin Shinkafi, Alhaji Muhammad-Makwashe Isah, game da hare-haren kwanan nan da kuma rasa rayuka, ya kuma kira ga goyon baya da hadin kai daga masarautar.
Kwamishinan, wanda ya sadu da shugabanni al’ummar yankin, ya yi alwashin gano da kuma hukunta wadanda suka aikata laifuffukan, ya kuma yi alkawarin karfafa harakar tsaro a jihar.
Idan dai baku manta ba a makon da ta gabat Labaran Duniya.Com ta ruwaito cewa ‘yan bindigar da ba a san su ba sun kai hari kan wasu garuruwa da ke yankin kananan hukumomin Shinkafi da Maradun a ranar Juma’a da Asabar da ta gabata, inda suka kashe mutane da dama.
Comments
Post a Comment