Najeriya C

Gwamnatin Najeriya ta bukaci cibiyoyi masu zaman kansu dasu hada kai da jami’an gwamnati na kiwon lafiya domin yaki da zazzabin cizon sauro.
Likitoci a Najeriya, sunce yanzu an daina amfani da tsofaffin magunguna irin su Chloroquine da Fansidar wajen maganin zazzabin cizon sauro domin sun daina tasiri.

Yanzu dai an kawo sabuwar kwayar maganin yaki da maleriya ta ACT, wadda babban sinadarin cikinta shine Artemisinin, dake taimakawa wajen rabuwa da wannan cuta da sauro ke haddasawa. Jami’in yaki da Malaria na Najeriya, malam Abdu Muhammad, yace yara talatin (30) ke mutuwa a a cikin ko wani sa’a daya a Najeriya sanadiyar zazzabin cizon sauro.

Hukumar yara ta Majalisar Dinkin Duniya, tace duk wuni malaria na kashe yara ‘yan kasa da shekara biyar su dubu biyu da dari uku a Najeriya, abinda yasa Najeriya, ta zama kasa ta biyu a yawan mutuwar yara ‘yan kasa da shekaru biyar a duniya.
Jami’in yaki da zazzabin na hukumar lafiya ta duniya a Najeriya (WHO) Rex yace gara a dage ana yin rigakafin kamuwa da cutar ta hanyar amfani da gidan sauron da aka masa feshin magani domin samun kariya.

Kamfanin har-hada magungunan kashe kwari da ake kira Morten, ya baje magunguna da yake sarrafawa, ganin yadda sauro ya addabi al’ummar Najeriya. Jami’in kamfanin Raul Murgai, yace dole a hana yaduwar Sauron ta hanyar feshin magani.

Jami’an duba-gari na ba da shawarar rigakafin cutar ta hanyar amfani da gidan sauro da kuma tsaftace muhalli. Najeriya, ta samu nasarar rage illar zazzabin cizon sauro daga kashi arba’in da biyu cikin dari zuwa ashirin da bakwai cikin dari cikin shekaru hudu da suka wuce

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’