Nigeria: An Tsaurara Tsaro A Zaben Jihar Anambra






Ana gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya cikin tsauraron matakan tsaro.

Babu wurin da aka samu rahoton tashin hankali, yayin da jami’an zabe suke ci gaba da aikin tantance masu kada kuri’a a safiyar Asabar.

Jami’an tsaro sun ci gaba da sintiri a duk fadin jihar musamman a garin Onitsha, inda kungiyar da ke fafutikar ballewa daga Najeriya IPOB da kuma kungiyar MOSSOB suke da karfi.

Jam’iyyu 37 ne za su fafata a wannan zabe mai cike da cece-ku-ce, ko da yake ‘yan takarar jam’iyyu biyar ne suka yi fice wato:

Tony Nwoye na APC

Gwamna Willie Obiano na APGA

Oseloka Obaze na PDP

Godwin Ezeemo PPD

Osita Chidoka na UPP

Wasu mazauna garin Akwa babban birnin jihar Anambra su sun ce shirye-shirye sun kammala ta fuskar gudanar da zaben da batun sha’anin tsaro da dai sauransu.

Sai dai sun ce IPOB ta rika yada takarda da ke cewa “zabe ba zai gudana ba” .

Kugiyar ta kuma nemi mutane akan su zauna a gida, kada su fita.

Wakilin BBC ya ce zaben zai kasance zakaran gwajin dafi ga jam’iyyar APC mai mulki a yankin kudu maso gabashin kasar.

A farkon makon nan ne Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyara yankin inda ya kaddamar da wasu ayyuka.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’