Harin Masallaci Yayin Sallar Juma’A Yayi Sanadiyar Mutuwar Mutum 54 A Masar
'Yan bindigar sun bude wuta a kan jama’a ne a wani masallaci dake arewacin yankin Sinai a kasar ta Masar.
Harin masallaci yayin sallar juma’a ya yi sanadiyar mutuwar mutum 54 a Masar
Hakazalika gidan talabijin din ya ce fiye da mutane 75 sun samu raunuka.
Ana cigaba da kokarin ceto mutanen da harin ya ritsa da su a masallacin.
Zamu kawo ma ku karin bayani a kan Hari da zarar mun samu karin rahotanni daga majiyar mu.
Ana samun yawaitar kai hare-hare a wuraren ibada domin idan ba ku mance ba ko cikin satinnan mai karewa saida wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan masallata a wani masallaci dake Garin Mubi ta jihar Adamawa.
Comments
Post a Comment