Fadar Shugaban Kasa Ta Bayyana Abin Da Buhari Ya Tattauna Tare Da Shuagabannin Addinan Kirista Da Musulunci







A ranar Juma’a ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya tabbatar wa shuwagabannin addinai da sauran ‘yan Najeriya cewan gwamnatin sa za ta magance mastalolin cin hanci da rashawa, almundahana, rashin adalci da rashin tsaro a sassan Kasan nan.

Ya yi wannan jawabi ne yayin tarban wakilan al’ummar kirista da na musulmi, a lokuta mabambanta na ranar, karkashin jagorancin shuwagabannin kungiyoyin addinan na CAN da JNI.

Buhari ya shaidawa wakilan CAN cewa ya bayar da umurnin a gabatar ma sa da sunayen shuwagabannin ma’aikatu da hukumomi domin bincike game da zargin daukan aiki ba bisa ka’ida ba.

Buhari ya kuma ba su tabbacin kawo gyara cikin harkar Hukumar ‘yan sanda da ta Shari’a. Ya ce da su ne za a samu tsaro da adalci da nutsuwa. Ya kuma yi kira ga ga shuwagabannin addinan da a hada karfi da karfe wurin magance almundahana da cin hanci da rashawa.

Don a cewar sa ga wakilan JNI, cin hanci da rashawa ya bi jinin ‘yan Najeriya, sai an yi taron dangi za a iya magance shi. Wakilan CAN sun yabawa Buhari kan aikace-aikacen sa, a inda su kuma wakilan JNI su ka roke ji da ya kara himma, kuma ya cigaba da jin tsoron Allah.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’