Kasafin 2018: Buhari Na Shan Raddi Game Da Bawa Fanin Ilimi Kashi 7

Kasafin 2018: Buhari Na Shan Raddi Game Da Bawa Fanin Ilimi Kashi 7





Kungiyar Kare Hakkokin Musulmai (MURIC), ta yi Allah wadai da kashi 7 da a ka ba wa fanin ilimi a kasafin 2018 da Buhari ya gabatar ma Majalisa. Shugaban Kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, shi ne ya bayyana hakan a Ranar Laraba.

Kungiyar ta yi nuni da cewan sakamakon halin ko-in-kula da wannan gwamnatin da gwamnatocin baya su ka yi ga harkar ilimi, ya sa harkar ta tabarbare. Ya isa misali yadda kashi 70 na dalibai sun kasa cin jarabawar shiga makarantun gaba da sakandare na 2017/2018.

Haka dalibai ke fadi warwas ko wace shekara, in banda 2016 da a ka samu kashi 50 da su ka ci. Shi ma din ba wani abun alfahari bane, in ji kungiyar. Don kuwa Kungiyar Kula da Ilimi da Kimiyya da Al’adu na Majalisar Dinkin Duniya, (UNESCO), ta shawarci ba wa ilimi kashi 26 na kasafi.

Ita kuwa Najeriya ko yaushe sai dai ta yi kunnen uwar shegu ga wannan shawara, ba a taba samun kaso mai tsoka ba, ballanta wanda ya kai kashi 26. A cewar kungiyar, ta yaya kuwa za’a samu cigaba a harkar ta ilimi.

Kungiyar ta kalubalanci Gwamnatin Tarayya da ta yi gaggawan kawo gyara da kuma sanya takunkumi a lamarin, ta yadda za a hana jami’an gwamnati da ‘yan siyasa tura ‘ya’yan su kasashen waje neman ilimi.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’