Za a Yiwa Malaman Makaranta Jarrabawa A Jihar Bayelsa
Yanzu haka ana shirin yi wa Malaman Makarantun Firamare da Sakandare gwaji a Jihar Bayelsa kamar yadda mu ka samu labari a jiya.
Gwamna Dickson zai fito da jarrabawar Malaman Makaranta
Gwamnan Jihar Bayelsa Seriake Dickson ya bayyana cewa za a yi wa Malaman Makaranta jarrabawa a fadin Jihar kuma za a kawo wani kudiri a Majalisar dokokin Jihar da zai sa a rika yi wa Malaman Jihar irin wannan jarrabaw.
Dole dai kowane Malami sai ya rubuta wannan jarrabawa inji Gwamna Dickson inda yayi wannan jawabi ta bakin mai magana da yawun sa watau Francis Agbo a jiya Laraba wajen wani taro da aka yi a Babban Birnin Jihar na Yenagoa.
Agbo yake cewa Majalisar dokokin Jihar Bayelsa na nan tafe da wani kudiri da zai sa a rika yi wa Malaman Makarantun Firamare da Sakandare jarrabawa kafin a dauke su aiki domin ganin an gyara harkar Malanta a fadin Jihar.
Comments
Post a Comment