Jam’Iyyun APC Da PDP Sun Yi Na’am Da Tsayawa Takarar Shugaba Buhari A Zaben 2019 – Rochas Okorocha



Yayin ganawa da kungiyar matasan dimokuradiya a ranar Talatar da ta gabata a fadar gwamnatin jihar dake birnin Owerri, Okorocha ya bayyana cewa, in banda biyu ko uku, dukkanin gwamnoni na jam’iyyu biyun suna goyon bayan sake tsayawa takara na shugaba Buhari a zaben 2019.

A wata sanarwa ta Okorocha da sanadin sakataren gwamnatin jihar mai hurda da manema labarai, Sam Onwuemedo ya bayyana cewa, Ina da cikakken yakini akan shugaba Buhari kuma na zamtowar shi gwarzo wanda zai juyar da akalar shugabancin kasar nan, duba da tarihin da ta tara.

“Babu mutum mafi dacewa da shugabancin Najeriya irin Buhari. Babu lallai a shekarar 2023 ko 2027 ya zamto mafi dacewa, amma a halin da Najeriya take ciki shine kan gaba wajen dacen shugabancin ta.”

Rochas Okorocha tare da Shugaba Buhari
“Yakar cin hanci da rashawa ba karamin aiki bane wanda sai irinsu Buhari ne kadai zasu jure. Tsare-tsaren sa ya sanadin kawo karshen ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas, wanda shi kan shi wata jarumta ce ta dab

“Najeriya ta fito daga matsin tattalin arziki cikin kankanin lokaci wanda hakan ya shiga tarihin duniya, kuma duk wannan shi yake nuna irin nagartar shugaba Buhari. Sakamakon haka ne ya sanya na ajiye muradin shugabancin kasar nan saboda na mara masa baya.”

Yayin mayar da martani ga jawaban Okorocha, Sakataren jam’iyyar PDP na kasa Prince Dayo Adeyeye ya bayyana cewa, “gwamnonin mu ba su wata alaka da tsare-tsaren tsayawa takara na shugaba Buhari. Mun riga da mun shafawa Rochas fenti na karairai, saboda haka kar wanda ya dauke shi da muhimmanci.”

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’