Muna Kokarin Tura Malaman Makarantan Da Muka Sallama Wasu Wurare – Inji Gwamnan Kaduna
Mun samu labari cewa Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai na shirin jefa Malaman Makarantar da ya sallama kwanan nan zuwa wasu fannin na dabam.
Ku na da labari cewa Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya sallami Malaman makaranta sama da 20,000 kwanan nan bayan sun fadi jarrabawar ‘yan firamare. Sai dai Gwamnan yace yana duba inda zai jefa wadannan Malaman a Jihar. Gwamnan zai dauki wasu sababbin Malamai a Jihar kwanan nan.
Gwamnan ya bayyana haka ne ta shafin sa na Tuwita a jiya bayan da wani Mutumi Bashir Muzakkar ya nemi ya ba Gwamnan shawarar yadda ya dace ayi da Malaman da aka kora. Gwamnan yayi na’am da wannan ya kuma nemi ya turo masa shawarar sa a sakon Email domin ya duba.
Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa tun da su ka hau mulki su ke kokarin ganin yadda za ayi game da harkar ilmi a Jihar Kaduna. Gwamnan dai ya nemi duk wata mai shawara ya aiko masa ta akwatin kamar yadda ku ka ji. Da dama dai sun yi kira a nemawa Malaman wnai aikin.
Comments
Post a Comment