Wani Saurayi Daga Najeriya Ya Zama Gwani A Wajen Gasar Rubutu,



Yanzu haka an samu wani Matashi daga Yankin Arewacin Najeriya da yayi zarra a Gasar rubuce-rubuce da aka yi na tsawon rabin shekara a Najeriya da kuma Kasar Kamaru.

Sada daga Garin Malumfashi ya samu damar zuwa Turai
Wani gasa ne da aka fara tun tsakiyar shekarar nan a Garin Limbe na Kasar Kamaru wanda a karshe Sada ya zo na daya kwanan nan a Garin Abeokuta cikin mutane kusan 10. An hora wadanda su ka shiga gasar na wata da watanni inda a karshe aka zabi wanda yayi zarra.

Bayan an dauki dogon lokaci ne dai Sada ya ciri tuta inda ya zo na farko a Najeriya. Hakan ta ba Matashin marubucin damar zama a Kasar Jamus na watanni 3 a karkashin gidauniyar Sylt ta Turai kamar yadda mu ka samu labari. An kuma zabi wanda yayi nasara daga Kamaru.

Malam Sada Malumfashi yana zama ne a Garin Kaduna amma asalin mutumin Kudancin Jihar Katsina ne. Ko da dai Sada ya karanta ilmin sarrafa magunguna ne a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya ya koma fagen rubuce-rubuce kamar mahaifin sa Farfesa Ibrahim Malumfashi.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’