An Tsinci Gawar Dan Jaridar Daya Bata A Anambara
‘Yan sanda sun tsinci gawar wani dan jarida ma’aikacin Anambara Broadcasting Service mai suna Ikechukwu Onubogu bayan kwana hudu da iyalan sa suka shigar da kara a wajen ‘yan sanda cewa ya bata basu gan shi ba.
‘Yan sandan Najeriya
Har yanzu dai ba’a tantance menene ya janyo ajalin nasa ba. Matar sa ta ce suna gida sai aka kira shi a waya a ranar 12 Nuwamba da rana; bayan nan ya dauki kyamarar sa ya fita; daga nan bai sake dawowa ba.
‘Yan sanda sun tsinci gawar a Obosi, kusa da Onitsha. A yanzu haka sun mika da gawar zuwa Asibitin Koyarwa na Amaku, da ke Awka,
Da aka nemi ji daga bakin shugaban ABS Uche Nworah, ya ce, “Mista Onubogu mutumin kirki ne kuma ba’a san shi da hayaniya ba. Babu yadda za’a yi mutum yai zaton wasu zasu yi masa haka.
“Duk ma’aikacin ABS ya yi jimamin mutuwar nan saboda Onubogu na da hazaka wajen aiki. Ga shi da kurdakurda wajen iya nemo labarai.
“Muna yi wa iyalin sa jaje, musamman matar sa da ta haihu a kwanannan.”
Ya gama da cewa wannan mutuwar ta nuna cewa rayuwar dan jarida kullum tana cikin hatsari saboda shige-da-ficen nemo labarai.
Mai magana da yawun bakin ‘yan sandan jihar, Nkeiru Nwode, ya gaskata aukuwar wannan lamari, kuma ya yi wa iyalan Mista Onubogu jaje, da kuma cin alwashin ‘yan sanda baza su yi kasa a kafa ba sai sun binciko wadanda suka aikata wannan aika-aikar don a hukunta su.
Comments
Post a Comment