Masu Neman Shugabancin PDP Zasu Rattaba Hannu A Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Ranar Talata – Inji Dokpesi






Jigo a jam’iyyar adawa ta PDP, Cif Raymond Dokpesi kuma daya daga cikin ‘yan takarar neman shugabancin jam’iyyar, ya ce dukkanin masu neman takara su 8 za su rattaba hannu a yarjejeniyar zaman lafiya a matsayin wani ɓangare na samun nasara a babban taron da za a yi a watan Disamba.

Dokpei, wanda ya kafa kamfanin Daar Communications, ya bayyana wannan a cikin wata hira da manema labarai bayan taro inda kungiyar gwamnonin PDP ta gana da dukan masu neman takara a Enugu, wanda aka kammala a safiyar yau Litinin.

Kamar yadda majiyar mu, ke da labari , Dokpesi ya bayyana cewa duk masu neman takara sun amince da su shiga yarjejeniyar zaman lafiya a babban sakatariyar jam’iyyar, Wadata Plaza, wanda ke birnin Abuja a daidai karfe 4 na yamma.

Ya ce ‘yan takara sun amince suyi aiki tare.

Gwamnan jihar Ekiti kuma shugaban kungiyar gwamnonin PDP, Mista Ayodele Fayose ya bayyana cewa taron koli na kasa, wanda za a gudanar a ranar 9 ga watan Disamba, zai zama wata abin koyi ga sauran jam’iyyun siyasa.

Wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban jam’iyyar, sanata Ahmed Makarfi da duk gwamnonin PDP sun halarci taron, sai dai gwamnan jihar Ebonyi ya tura wakilinsa.

Sauran masu neman shugabancin PDP a taron sune, Cif Bode George, Gbenga Daniel, Prince Uche Secondus, Farfesa Tunde Adeniran, Jimi Agbaje, Taoheed Adedoja da kuma Rashid Ladoja.

Cikin wadanda suka kuma halarci taron, sun hada da Ike Ekweremadu, mataimakin shugaban majalisar dattawa da Gabriel Susuwan, tsohon gwamnan jihar Binuwai da Adolphus Nwabara da kuma Sule Lamido.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’