Yan kasuwa Sun Zubar Da Hawaye Yayin Da Gobara Ta Kama Shaguna A Birnin Akure
A ranar Talatar da ta gabata ne ‘yan kasuwar suka rinka zubar da hawaye yayin da suke bayyana irin asarar da suka tafka sakamakon wannan gobara da afku da misalin karfe 2:00 na dare a babbar hanyar Roadblock dake daura da wurin sayar da abinci na Chicken Republic.
‘Yan kasuwa sun zubar da hawaye yayin da gobara ta kama shaguna a birnin Akure
Labaran majiyar mu. ta ruwaito da sanadin jaridar Daily Trust cewa, wannan gobara ta afku ne sakamakon wata ‘yar matsala ta wutar lantarki, inda mazauna yankin suka yi iyaka bakin kokarin su na kashe wutar bayan ta debi awanni tana aika-aika a shagunan kafin zuwan ‘yan kwana-kwana.
Dukiyoyi na tarin miliyoyi sun salwanta a cikin shagunan da wannan gobara ta lashe, inda ‘yan kasuwar suka bayyana cewa mafi akasarin hajojin su sababbi ne da suke shirin cin kasuwar bikin kirsimeti da kuma sabuwar shekara.
Comments
Post a Comment