Batan-Baka-Tan-Tan: Jam’Iyyar PDP Ta Sarewa Atiku Gwiwa Game Da Batun Takarar Sa A 2019
Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta yi tsokaci a game da batun ficewa daga jam’iyyar APC da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma fitaccen dan siyasa, Alhaji Atiku Abubakar inda ta bayyana shi a matsayin wani mai ‘yanci a yanzu.
Sai dai kuma jam’iyyar a cikin wani zance mai kama da na sare gwiwa, ta bayyana cewa tikitin ta na takara a zaben 2019 mai zuwa ba na kowa bane don haka ba zai same shi ba hakanan kai tsaye sai yayi takarar neman sa.
Majiyar mu, dai ta samu cewa a cikin sanarwar da jam’iyyar ta PDP ta fitar, ta bayyana cewa hakika Allah ne ya nufi tsohon mataimakin shugaban kasar da shiriya shine babban dalilin da yasa ya fita yabar jam’iyyar.
Daga nan ne kuma sai jam’iyyar ta mika sakon gayyata ga duk wanda yake ganin ba’a yi masa adalci a jam’iyyar ta APC da ya garzayo a jam’iyyar tasu domin su jam’iyyar su jam’iyya ce mai adalci ga kowa.
Comments
Post a Comment