Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri
Kungiyar ta gindayawa shugaban kasa sharadi da cewar, in har yana son goyon bayan su a zaben 2019 to sai ya sauya kujerar da mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo yake kai a yanzu da wani dan kabilar su na yankin Kudu maso Gabashin kasar nan
Majiyarmu ta fahimci wannan sharadi ya zo ne bayan da shugaba Buhari ya yanke shawarar ziyartar jihohin Kudu maso gabashin kasar a makonnin da suka gabata.
A wani rahoto da sanadin shugaban kungiyar Chilos Godsent da ya bayyana a birnin Owerri na jihar Imo, ya ce wannan ita kadai ce hanyar da jam’iyyar APC za ta samu goyon bayan su a zaben kasa na 2019.
Godsent ya kara da cewa, jam’iyyar APC ta maishe da yankin na su saniyar ware wajen gudanar da shugabancin ta a kasar.
Comments
Post a Comment