RA'AYIN NURA MAI APPLE A KAN KORAR MALAMAI DA GWAMNAN JIHAR KADUNA, MALAM NASIR YAR RUFA'I YAKE SHIRIN YI!




Assalamu Alaikum.

Barka da wannan lokaci mai Albarka da fatan mai karatu yana Cikin koshin lafiya,

Ko shakka babu, yunkurin da gwamnan jihar Kaduna yake shirin yi,  na korar wasu daga cikin masu Aikin malanta har kusan Dubu Ashirin da biyu(22,000)wani babban abin koma baya ne,  kuma da tir da Allah waddai ne.


Shin meyasa gwamna Malam Nasir Yar Rufa'i.  Wannan aika-aikar.  Domin kuwa inada  matukar yakinin cewa a cikin wadan nan bayin Allah akwai masu mata sama daya, haka akwai masu 'ya 'ya samu da daya.  To ashe kuwa inhar haka ne!   Suna da wadanda suke ci a karkashin su, adadin lunkin balunka,  shin baya tunanen  iyalan  wadan nan bayin Allah zasu iya shiga cikin wani mawuyacin hali.

Shawarar Nura mai Apple  a nan shine!


Babbar shawara ta nan shine, duk Wanda ankace bai iya abu ba,  to meyake bukata`` babban abunda yake bukata a nan shine a jajirce wajin koyamasa abin har ya'iya kuma yasan me ake nufi da abun,  kuma ya fahimce shi,


Shin koko  Gwamnan Jihar Kaduna malam Nasir.  Ya samama su wadannan bayin Allah wani aikin yi ne?


Idon kuma mai girma gwamnan jihar kaduna malam nasiru yar Rufa'i,  ya samama su wadannan bayin Allah aiki yi,  to yana da damar korar su.  Domin maye gurabun su da wasu, wadanda sunka samu huron koyarwar na musamman.  Su kuma  wadanda ake shirin kora to wajibi ne ga mai girma Gwamna da yasa mamusu wani aiki na daban.  Ina ganin kamar haka shine mafita kuma shine zaman lafiya da kwanciyar hankali.


Daga : Nura Muhammad Mai Apple Gusau.  Dan Kungiyar muryar talaka ta kasa. -----08133376020--

Nuramuhammad3337@gmail.com

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’