Skip to main content

Fursunoni Mata Na Karuwa A Duniya

Fursunoni Mata Na Karuwa A Duniya




Wani bincike da aka gudanar a kan yawan mata da ‘yammatan da ke zaman gidan yari a sassan duniya daban-daban, ya gano cewa adadin matan ya karu musamman a shekarun baya-bayan nan.

Binciken ya kiyasta cewa yanzu haka akwai mata fiye da dubu dari bakwai da ke zaman gidan gidan kaso a duniya.

A cewar wata cibiyar da ke bincike kan manyan laifuka da ke birnin London, adadin matan da ke zaman gidan kaso na karuwa a kowacce nahiya a cikin shekaru 17 da suka wuce, kuma an fi samun karuwar adadin fursunoni mata ne a kasashen Brazil da Indonesia da Phillipines da kuma Turkiya.

Cibiyar ta ce, inda kuma ake da yawan fursunoni mata su ne Amurka da kuma China.

An daure matar da ce mata na iya haihuwa babu aure

‘Mata ba za su yi daidai da maza ba nan da shekara 100’

A shekarar 2015, China ta samu karuwar fursunoni mata da yawa wadanda suka aikata laifukan da suka hadar sa sarafar miyagun kwayoyi da kuma cin hanci inji cibiyar.

Hakan ya sa China ta zamo kasa ta biyu a duniya da ta ke da yawan fursunoni mata.

To amma duk da haka yawan fursunoni mata na China bai kai rabin fursunoni matan da ke Amurka ba.

Kuma wadannan fursunoni wasu na zaune ne kafin a yanke musu hukunci, yayinda wasu kuma ke zaman hukuncin da aka yanke musu.

Masu bincike sun ce ana kashe makudan kudade wajen kula da fursunoni mata, to amma duk da haka baya wani tasiri ko kadan idan sun dawo cikin al’umma.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Masana sun ce daga cikin abubuwan da suka sa dan Adam yin galaba a kan sauran halittu shi ne yadda yake iya hada kai. Don mutum shi kadai ba zai iya gwada karfi da zaki ko giwa ba. Amma idan ya hada karfi da sauran ‘yan uwansa babu kalubalen da ba za su iya tinkara ba. Hadin kai kuma ba ya tabbata sai da yarda, kuma yarda sai da mu’amala. Masu hikimar magana sun ce, Allah Ya halicce mu da kunne biyu, ido biyu amma sai ya yi mu da baki daya domin mu kalla, mu kuma saurara fiye da yadda muke magana.  Amma sai ya kasance cewa mun fi son yin magana fiye da saurare. Sau da yawa idan muna tattaunawa da wadansu ba ma mayar da hankali kan abin da ake fadi. Kawai jira muke mutum ya kai aya - idan ba mu katse shi ba kenan, domin mu fadi namu ra’ayin. Ga shi kuma ba mu son jin ra’ayoyin da suka sha bamban da namu. To ina za a samu fahimtar juna har a yi aiki tare?  Babu wanda rayuwarsa iri ɗaya da ta wani, kowa da irin  jarabawar shi,  kowa kuma da irin ta shi f...

LABOUR ROOM BLOBAL INITIATIVE KIRA NA MUSAMMAN ZUWA GA MATASA DA 'YAN SIYASA

Duk tarin dukiyarka, ko girman mulkinka ko zamanka basarake, ba zaka taɓa jin daɗin abinda kake taƙama da shi ba, matuƙar al`ummar da kake rayuwa a cikinta ba su zaune lafiya ko da kai ka tsira, kuwa. Shi dama talaka juji ne, duk wani tarin dattin tashin hankali, akansa yake ƙarewa. Da shi ake amfani wajen tashe-tashen hankula, shi ke kisa kuma shi ake kashewa kuma duk masifar da kan biyo baya a kansa ne take sauka. In ko haka ne, haƙiƙa da sake! kenan kowa na matuƙar kaunar zaman lafiya a cikin al'umma, domin sai da zaman lafiya ɗin ne, kowa zai iya morewa, har ya iya rayuwarsa ba tare da shiga tasko ba. A kan haka ne! Ƙungiyar Labour Room Global Initiative haɗin gwiwa da Ƙungiyoyin Jihar Zamfara ke amfani da wannan damar wajan kira ga dukkanin 'yan Siyasa, da ayi siyasa ba tare da gaba ba. Domin in dai har za'a iya zubar da jini a kashe rai a zaɓen fitar da gwani kurrum na jam'iyya ɗaya, to ina ga zaɓen gama-gari da ke tafe? Don haka muna amfani da wannan ...

A SAMARWA DA 'YAN GUDUN HIJIRA DA MASAUKAI!

A bisa ma'aunin Ilimi da hangen nesa, duk wanda ya baro garinsu, inda komai nasa a ce yake, kamar 'yan Uwansa da abokansa, mahaifansa, wadanda suke a raye da kuma wadanda Allah yayi rasuwa, kuma ya baro abincinsa wanda zaici, ya baro dabbobinsa wadanda ya dogara da su, Kacokan! ya fantsama yayi kaura zuwa wani waje, inda shima kansa bai san inda ya maida gaba ba, ina ganin wannan shine mafi munin tashin hankali da firgici da ɗimauta. A kullum a duk inda ka duba zakaga 'yan gudun Hijira ne birgik a saman tituna suna yawon barace-barace cikin kaskance da takaici, musamman yara 'yan Dagwai-dagwai wasunsu ma basu dade da fara iya tafiya ba, suna neman a taimake su, da abinda zasu ci, wasu daga cikinsu ko takalmin sakawa basu da haka nan suke yawo a Kasa cikin tagaiyara da nadama. Haka idon mukayi la'akari da yadda idon mutun ya saba da wajen zamansa akace ya tashi yabar wurin ba tare da kintsawa ba, yaya yake ji a cikin ransa? A 'yan baya-bayan nan shekaru biy...