Yanzu-Yanzu: Hukumar JAMB Ta Tsaida Ranar Da Za’A Rubuta Jarrabawar 2018
A safiyar yau Laraba ne hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandiri JAMB ta bada sanarwan cewa zata gudanar da jarabawar shekarar 2018 ne a daga ranar 9 – 17 na Mayun 2018.
Shugaban hukumar Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bada sanarwan a wani taron masu ruwa da tsaki a fanin ilimi. Yace an tsayar da ranakun jarabawar ne bayan anyi la’akari da ranakun da dalibai zasu rubuta wasu jarabawan.
Ya kara da cewa hukumar zata gudanar da jarabawar gwaji daga 22 ga watan Janairu zuwa 27 na watan duk dai a shekarar 2018 din. Har ila yau, yace kudin rubuta jarabawar JAMB din yana nan kamar yadda aka sani N5000.
Comments
Post a Comment