Talakawa na buƙatar Tallafi
Kasancewar kowace shekara idan irin wannan lokaci ya kama, malamai hadi da dai-dai kun jama'a suna cigaba da kiraye-kiraye domin tallafawa al'umma musamman masu dankaramin karfi. To babu ko shakka, zamu iya cewa kowace shekara akwai sauki sosai idan muka kamanta ta da shakarar bana, domin kuwa ba talakawan ba har masu kudin suna jin a jikinsu, idan muna dubi yadda komai ya tsaya cik sakamakon cutar annobar korona wanda ta addabi duniya baki daya. Duk da haka, kasancewar sai da ruwan ciki ake janyo na rijiya, akwai bukatar masu hannu da shuni da su dubi girman Allah su taimakawa al'umma, domin ana cikin halin kuncin rayuwa, a bangarori daban-daban na sassan ƙasar nan. Babu yadda za'ayi mu samu cigaba ta kowane fanni sai in ya kasance mun sanya tausayi ga na kasa damu. Tun cen dama Najeriya tana cikin halin matsi tun kafin zuwan wannan lokaci wanda kuma mafi yawa daga cikin al'ummar ƙasar sun san haka, fatan 'yan uwanmu masu hannu da shuni, 'yan kasuwa...