SHIN KO YAZEED NA DA RA'AYIN SIYASA?
_mutane da dama suna irin wannan tambayar musamman irin yadda sun ka ga ya himmatu wajan ayyukan alheri a cikin al'umma, abu ne baƙo a cikin jama'a su ga ana irin wadannan ayyuka a yankunansu, ko da kuwa ga 'yan siyasa ne masu rike da madafun iko, hadi da wadanda basu rike da wata kujera, yan siyasa da ma'aikatan gwamnati. Wannan ne ya sa; shugaban mai kula da gidauniyar (Alh, Yazeed Shehu Dan fulani, Comrade Rufa'i Bala UB) ya zan ta da manema labarai a wata hira da gidan TV na Maibiredi tayi da shi a jiya juma'a 03/04/2020, domin yiwa al'umma bayani akan manufar Alh, Yazeed Shehu Danfulani Mai Doya._
_Mai tambaya ya masa tambaya kamar haka; Assalamu alaiku, Malam Rufa'i Bala UB akwai wata tambaya da muke so mu yi maka a kai, wanda ya shafi tafiyar Yazeed Trust Fund musamman bisa ga ayyukan da muke ganin gidauniyar tana yi kuma al'ummar jihar Zamfara sun shedi haka, muna ji daga bakinku kuna cewa; tafiyar Yazeed Trust Fund bata siyasa ba ce, tafiya ce ta taimakon Al'umma, amma bayan haka mun tsintsi wasu Banas dauke da jam'iyyu, to kun dauki jam'iyya ne ko kuna son ku shiga siyasa ne? Muna son mu ji daga bakinka?_
_Sai Comrade UB ya mayar da amsar tambayar kamar haka ''Da sunan Allah mai Rahama Mai jin Kai, ina yiwa masu sauraro da masu kallo barka da juma'a Allah Ya bamu albarkacin da ke cikinta, alhakikanin gaskiya naji dadin wannan ziyara da kuka kawo min a Offishinmu na Yazeed Trust Fund wanda kuka nemi ku tattauna da ni akan abin kuke ganin ya shige maku, ko ya shigawa al'umma duhu, wadanda ya kamata na ansa maku su, wanda a farko ina mai baku hakuri kasancewar tun jiya kuke kokarin ganin kun tattauna da ni. Hakika tafiyar Alh Yazeed Shehu dan fulani mai Doya garkuwan matasan Gusau lamidon Tsafe kusan ince maku abin yazo daidai da lokacin da Allah madaukakin sarki ya kaddari al'ummar musulmi talakawa da marayu suji dadi sai Allah ya kawo masu Alh, Yazeed shehu dan fulani mai doya, Allah ya karfafa masa gwiwa akan abubuwan da yake kusan shekaru 10 da suka gabata, wanda ba zan manta ba, tun tashinsa dukkan wanda ya sansa ya kasance mutum mumini mai iya fitowa ya bada sheda zaka ji ya fara fadin kyawawan dabi'un Alh Yazeed Shehu Danfulani tun yana karaminsa kamar yadda wata tsohowa take kara jaddada mana cewa''. ''wannan yaro tun yana karami idan ta dauko shi sai kaji yana cewa shi dai Allah ya bashi kudi domin ya taimaki al'umma, cikin ikon Allah yanzu gashi Allah ya nuna mata Yazeed din nan dai wanda ke fadin
hakan yanzu Allah yasa shine al'umma ke ma tofin Allah sambarka, shine Al'umma ke yiwa fatan Alheri, ba tare da siyasa ba, ko la'akari da wani abu daban''. Saboda haka duk abinda kaga yana yi ba wani abu bane illa shauki da zimma''._
_Ya ce; '' akwai wata tsohuwa da (Alh, Yazeed) ya ginawa gida, bata sanshi ba, bata ma taba ganinsa ba, amma ya gina mata gida saboda Allah. Haka akwai marasa lafiya wadanda yayi wa lalurar 200,000, 300,000. Wadanda masu jinyar sun warke har sun fara tafiya a kasa, to kaga kenan dukkan wanda aka sanya wa farin ciki zai dauwama a ciki. Kamar mutum ne mai jin kishirwa, yana jin yunwa ka dauko abinci mai kyau wanda bai taba tunane ba ka bashi, ya ci, ya sha, ka mutunta shi, to zakaji ya na cewa da za'a iya yiwa sama Rafta zai iya buga mata kwano, wannan shine Bahaushe ke cewa Sonti!''_
_'' yau duk jam'iyyun da zaka gani, zaka ga kowa na yiwa Yazeedu fatan alheri ɗan jam'iyyar siyasa yake, ko wanda bai ra'ayin siyasa ne, amma har illa yanzu da nake magana, Alh, Yazeed Shehu bai fito ya furta maganar siyasa ba, sannan bai yi damu ba, kuma bai furta ma duk wani wanda yake da alaka ta kusa ko ta nesa hakan ba. Idan har za'a ji maganar shigarsa siyasa ko jam'iyya to ina tunanen cewa a nan cikin Yazeed Trust Fund ko wasu kungiyoyi wadanda ke da karfi na tare da Alh Yazeed Dan fulani za'aji wannan. Amma ba zaka hana mutum ya maka fatan alheri ba, kamar idan mutum ya ce Allah ya maka shugaban kasa kaga ni bazan fito na ce ba Amin ba! har yanzu ina kara jaddada maku cewa babu wata siyasa ko jam'iyya ko wani abu na kishi tsakaninmu da wani dan siyasa ko abin da ya shafi lamarin siyasa, abi ne wanda kowa yasan Alh, Yazeed Shehu Dan fulani mai doya, ya gaji alheri ya taso cikin mutunta al'umma yana karfafa gwiwa wajan ganin anyi aikin alheri. Tun yana a makarantar boko zakaji abokan karatunsa suna masa kirari da ''fada'' saboda adalcinsa da rikon amana, kuma yanzu idan ka duba dukkan inda ya ke gyare-gyare musamman taimakon yara marayu inda ya sa masu suna da 'yara masu daraja', da kera riyoji, gyaran masallatai, ciyarwa a asibiti, mata masu yayon fitsari, daukar marasa lafiya, biyawa yara kudin karatu wadannan abubuwan duk suna a cikin tsarinsa. Saboda haka nake kara sanar daku cewa babu maganar siyasa sai dai ba zaka iya hana mai fata yayi fatarsa ba._
_Inda Comrade UB ya kara da cewa, Manzon Allah Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareSa ya Cewa; ''Mafi alheri a cikinku shine wanda Al'umma ke amfanuwa da shi'' to duk inda kaga mun bayyana to manufarsa ya za'ayi a kawo alheri a cikin al'umma, amma ba maganar siyasa ba. Wannan kenan''._
_A lokacin da aka kara jefa masa wata tambayar, inda mai tambayar yace; ' yanzu wane irin kira zakayi ga su masu biyar Yazeed ko masu masa fatan alheri da cewa su daina furta wasu kalamai wadanda basu dace ba ga takwarorinsa 'yan siyasa'?_
_Sai ya kara da cewa; ''eh Alhamdulillahi a shekaranjiya akwai shugabanninmu na Yazeed Trust Fund da wsu kungiyoyi daban-daban ke tafiya a cikin lemar nuna kauna da soyayya ga Alh Yazeed Shehu Danfulani, kiran da zanyi ga mutane shine; su yi mana adalci su yiwa Yazeed adalci, kar suje su furta wata magana ga wani akan Yazeed domin cewa idan muka auna bai taba fitowa ya ci mutuncin wani ba, hasali ma bai taba yin siyasa ko rike wata kujerar siyasa ba, bai da tashin hankali da kowa, kada ka dauki soyayyar da kake yiwa Yazeed yasa ka dau fansar wata hulda , idan lokacin siyasa yayi ba'a hana kowa yayi siyasa ba, sannan a cikin tafiyarmu ta Alh Yazeed"._
_A cikin tafiyar Yazeed Kowa ma akwai har 'yan baruwanmu akwai, sai dai muna kira da babbar murya ga duk mai kokarin yin suka ko wani abu na daban, ya shafawa kansu ruwa, ya shigo muyi wannan tafiyar dashi wanda zamuyi tarayya wajan gudanar ayyukan alheri, amma don Allah mu daina cin mutuncin wani, domin Alh, Yazeed a kullum kiransa shine ba ya son ya ga ana cin zarafin wani, baya son ma ya ga yana tarayya da kai kana cin zarafin wani, to ka ji irin kiran da zanyi kenan a takaice._
_A karshe sun tambaye shi wani irin kira zai yi ga 'yan uwa masu hannu da shuni da suyi ko'i da irin halayyar Alh, Yazeed Shehu Danfulani wajan taimakon Al'umma._
_Sai ya kara masu da cewar; '' tabbas shekaranjiya wani babba daga cikin masu juya jihar nan, ya kira ni yana jinjina min a kan kokarin da mukeyi, duk da muna 'ya'yan talakawa muna son mu zauna muji dadi amma a kullum muna fadi tashi ga masoya Yazeed ba su sa kudi a aljihu ba, sai dai suje domin su amfanar da al'umma, saboda haka kiran da zanyi shine, masu hannu da shuni, 'yan kasuwa dama 'yan siyasa su sani cewa addininmu ya riga ya koyar da mu, mu kyautatawa al'umma daidai kokarinmu. Sama da shekaru 10 da muka kwashe muna ayyukanmu na alheri ga al'umma, Alh Yazeed ya hana a bayyana sai yanzu da munka ci karfinsa, sannan ya fara barin ayyukan sun ka fara fitowa fili. Ya kara cewa wani babba a lokacin da ya kirayeshi a waya yana cewa kaga yanzu Rufa'i kunyi silar yanzu sanadiyar cutar nan mai sarke lunfashi ta Coronavirus, wanda muke fatan kar Allah ya kawo ta jihar nan, kuma muke fatan Allah ya kawo karshenta baki daya a kasaashen da sunka kamu da ita. Yake cewa ya ji dadi matuka irin yadda mun ka fara bayar da tallafi yanzu gashi al'umma sun bi sahunmu, hakika munji dadi sosai irin yadda muka ga al'umma sun fito suna taimakawa mabukata, sannan kasancewar akwai watan Ramadan zuwa, akwai masallatai sun yi shekaru babu fyanti akwai bukatar al'umma su taimaka wajan gyarasu. Yace akwai irin magudanan ruwa dake a cikin unguwanni masu bukatar agaji, yana da kyau al'umma su agaza domin ganin an gudu tare an tsira tare._
_A karshe yayi addu'ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Zamfara da Najeriya kwata._
*Daga Nura Mai Apple*
Comments
Post a Comment