ZIYARAR JAJANTAWA
Yazeed Trust Fund Team
YAZEED TRUST FUND
A daran jiya ne 10/04/2020 Wannan gidauniya mai albarka ta samu kai ziyarar jajantawa ga tsohon Shugaban ƙaramar Hukumar mulki na Gusau, (Alh Ibrahim Umar Tanko) domin jajanta masa a kan abin da ya faru da shi.
Dukkan waɗannan suna daga cikin jerin abubuwan wannan Gidauniya, a lokacin wannan ziyarar tsohon shugaban ya nuna farin cikinsa a bisa wannan ziyara sannan yayi godiya da yabo ga wannan gidauniya da masu tallafa mata, sannan yayi addu'ar Allah ya saka da mafificin alheri.
Ya jinjinawa shugaban Yara maso Daraja matashin dattijo, (Alh, Yazeed Shehu Ɗanfulani Garkuwan Matasan Gusau Lamidon tsafe)
Da fatan Allah ( S,W,T) ya tsare gaba ya sa wannan ya kasance kaffara a garesa.
Nura Mai Apple, Media Reporter.
Copyright©maiapple
Comments
Post a Comment