Majalisar Himma ta amfana da Tallafin Karatu, Daga Yazeed Trust Fund
Ilimi shine ginshiƙin kaiwa ga kowace irin nasara a rayuwa, kuma sai da shine sannan ɗan Adam ya kan iya bambanta kansa da dabba! Babu wata al'umma da zata cigaba a duniya matuƙar babu ilimi a cikinta, wannan ne yasa Gidauniyar Yazeed Trust Fund ta himmatu wajan tallafawa Yara da zimmar ƙarfafa masu gwiwa ta hanyar fafutikar neman ilimi.
Kamar yadda ta saba A yau 07-04-2020 Gidauniyar (Yazeed Shehu Danfulani Lamidon Tsafe Garkuwan Matasan Gusau) wato Yazeed Trust Fund da ke a babban Ofis a Gusau ta baiwa [Majalisar Himma] dake Tudun wada kyautar Fom 'Form' na ɗaukar nauyin marayu da Masu Rauni 20 a karkashin kungiyar domin saka su a makaranta
da ( Hon Alh Yazeed Shehu Danfulani) ya dauki nauyi a cikin shirinsa na YARA MASU DARAJA.
Shugaban Yazeed Trust Fund (Comrade Rufai Ub Gusau Salanken Galadima) shine ya kaddamar da bada forms din a yau. Da yake mayar da jawabin godiya shugaban wannan kungiya tare da 'yan fadarsa sun yi farin ciki sosai da samun wannan dama, sannan yayi addu'ar Allah ya saka masa da mafificin alheri kuma ya shige masa a gaba ga dukkan lamurransa.
Haka ya jinjima shugaban Gidauniyar Yazeed Trust Fund tare da abokan hidimarsa. Da suke dafa masa baya wajan gudanar da ayyukan alheri a cikin al'umma.
Comments
Post a Comment