Taya murnar bikin Aure
Mun samu damar halartar addu'ar daurin auren Abdul'aziz Salisu Meelo. Daurin auren dai ya samu halartar muhimman mutane da dama a sassa daban-daban a yankuna da dama, daga ciki har da 'yan uwa ma'abota amfani da kafafen zamani Social Media a taƙaice.
Daurin auran ya gudana a bakin Sinima, ƙofar Yarima cikin gundumar yankin mayana a nan ƙaramar hukumar mulkin Gusau a jihar Zamfara. Aure dai wata babbar turba ce kuma ginshiƙi ne na kaiwa ga kowane irin matakin nasara a rayuwa.
Hon Muhammad Salisu Meelo shine ƙane ga ango, kuma ta sanadiyarsa ne mun ka samu damar halartar wannan ɗaurin Aure, bikin dai ya gudana cikin nastuwa da kwanciyar hankali.
Saura da mi muna fatan Allah ya sanya albarka da alheri a cikin wannan aure, Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a ta gari.
Daga Nura Mai Apple, Media Reporter.
Copyright©maiapple
Comments
Post a Comment