Skip to main content

Matasan Ɗan Bedi sun nemi haɗin gwiwa wajan ayyukan alheri da Yazeed Trust Fund

YAZEED TRUST FUND MEDIA


  A cikin kowane lokaci wannan tafiyar tana kara samun tagomashi, inda cikin ikon Allah wasu zaratan matasa da dattawa suka yi haɗin  gwiwa ga tafiyar matashin dattijo (Alh Yazeed Shehu Ɗanfulani garkuwan matasan Gusau Lamidon Tsafe)  ko shakka babu a cikin kowace tafiya ana son samun mutum kamilalle irin Alh Yazeed, kasancewarsa mutum mai son ganin mutane cikin walwala da kwanciyar hankali, domin sai al'umma suna cikin walwala ne sannan zasu samu damar gudanar da lamurran yau da kullum.



Idan mukayi la'akari da a kowane lokacin faɗi tashinsa shine bayar da tallafi ga masu ɗan ƙaramin karfi, a Bisa duba da irin ayukkan alherin da yake yi don ganin ya kawo ma Al'umma sauyin rayuwa, wannan ne yasa wadannan matasa sun ka ga dacewar tuntuɓa domin ganin su kansu sun bayar da kowace irin gudunmuwa a cikin wannan tafiya, ta Alh Yazeed Shehu Ɗanfulani. 


Matasan haɗi da dattawan,  sunyi alkawarin zasuyi wannan tafiya ba tare da jin wani ɗar a zuciyarsu ba, domin suma sun haƙiƙance cewa zasu iya bada tasu gudunmuwa a cikin Al'umma don suyi koyi da wannan matashi Mai rikon amana.

A lokacin gabatar da nasa jawabin ga al'ummar yankin, shugaba mai kula da wannan gwagwarmayar samun cigaba (Comrd Rufa'i Bala UB Gusau) ya godewa Allah, kuma ya godewa al'ummar wannan yanki a bisa yin dogon nazari da hangen nesa da suka yi wajan ganin sun shigo an hadu waje daya don ciyar da al'umma dama jiha baki daya a gaba, a karshe yayi addu'ar Allah ya cigaba da zama gatan mai taimakon Al'umma a duk indan yake.

Da fatan Allah ya cigaba da daukaka garkuwan matasa ya kuma biya masa dukkan bukatunsa na alheri Don alfarmar manzon Allah ( S,A,W )

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Masana sun ce daga cikin abubuwan da suka sa dan Adam yin galaba a kan sauran halittu shi ne yadda yake iya hada kai. Don mutum shi kadai ba zai iya gwada karfi da zaki ko giwa ba. Amma idan ya hada karfi da sauran ‘yan uwansa babu kalubalen da ba za su iya tinkara ba. Hadin kai kuma ba ya tabbata sai da yarda, kuma yarda sai da mu’amala. Masu hikimar magana sun ce, Allah Ya halicce mu da kunne biyu, ido biyu amma sai ya yi mu da baki daya domin mu kalla, mu kuma saurara fiye da yadda muke magana.  Amma sai ya kasance cewa mun fi son yin magana fiye da saurare. Sau da yawa idan muna tattaunawa da wadansu ba ma mayar da hankali kan abin da ake fadi. Kawai jira muke mutum ya kai aya - idan ba mu katse shi ba kenan, domin mu fadi namu ra’ayin. Ga shi kuma ba mu son jin ra’ayoyin da suka sha bamban da namu. To ina za a samu fahimtar juna har a yi aiki tare?  Babu wanda rayuwarsa iri ɗaya da ta wani, kowa da irin  jarabawar shi,  kowa kuma da irin ta shi f...

LABOUR ROOM BLOBAL INITIATIVE KIRA NA MUSAMMAN ZUWA GA MATASA DA 'YAN SIYASA

Duk tarin dukiyarka, ko girman mulkinka ko zamanka basarake, ba zaka taɓa jin daɗin abinda kake taƙama da shi ba, matuƙar al`ummar da kake rayuwa a cikinta ba su zaune lafiya ko da kai ka tsira, kuwa. Shi dama talaka juji ne, duk wani tarin dattin tashin hankali, akansa yake ƙarewa. Da shi ake amfani wajen tashe-tashen hankula, shi ke kisa kuma shi ake kashewa kuma duk masifar da kan biyo baya a kansa ne take sauka. In ko haka ne, haƙiƙa da sake! kenan kowa na matuƙar kaunar zaman lafiya a cikin al'umma, domin sai da zaman lafiya ɗin ne, kowa zai iya morewa, har ya iya rayuwarsa ba tare da shiga tasko ba. A kan haka ne! Ƙungiyar Labour Room Global Initiative haɗin gwiwa da Ƙungiyoyin Jihar Zamfara ke amfani da wannan damar wajan kira ga dukkanin 'yan Siyasa, da ayi siyasa ba tare da gaba ba. Domin in dai har za'a iya zubar da jini a kashe rai a zaɓen fitar da gwani kurrum na jam'iyya ɗaya, to ina ga zaɓen gama-gari da ke tafe? Don haka muna amfani da wannan ...

MUNA JIMAMIN RASHIN 'YAR ADU'A

hakika tarihi ba zai taba mantawa da tsohon shugaban Kasar Najeriya ba, margayi Alh Umar Musa 'yar Adu'a, kasancewarsa duk da baiyi wani dadewa ba a kan karagar jagorancin kasar nan, amma Najeriya ta shedi gwagwarmayarsa, ta fannoni da dama. Idan muka yi la'akari da yadda ya zage damtse wajan fafutikar ganin Najeriya ta zauna lafiya, musamman rikice-rikicen 'yan tawayen Niger-Delta da sauransu. Idan muka dubi fannin samar da ilimi wanda a nan sashen yayi rawar gani, haka a fannin kiyon lafiya da cigaban rayuwa. Lokacin Alh Umar Musa 'yar'adua yana shugaban kasa talakawa da dama sun dara, kasancewar yayi yunkurin ganin kasar nan ta samu cigaba ta kowane fanni. Muna fatan Allah yaji kanshi ya masa rahama ya sanya aljanna ta kasance makoma a gareshi. Najeriya tayi babban rashi. Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau 08133376020