JAJANTAWA HADI DA BAYAR DA TALLAFI.
Kai tsaye daga unguwar Tsauni inda Kungiyar nan Mai son ganin jin dadi haɗi da walwalar Al'umma, musamman masu neman taimako wato (YAZEED TRUST FUND) Karkashin Kulawar (Alh Yazeed Shehu Danfulani, Garkuwan Matasan Gusau, Lamidon Tsafe).
Yau ma kamar yadda ta saba yin halin nata na Alheri inda ta ziyarci Dan uwa Abokin gwagwarmaya (Saminu
Gajam) Domin jajanta masa a kan Ibtila'in gobara da ta samu gidansa Tare da bashi Tallafin kaya rage raɗaɗin wannan hali da yake ciki, sune kamar haka;
Kwanon Rufi Kwaya 40
Buhun Suminti 10
Shugaban jajirtattu (Comrd Rufa'i Bala UB shi ne; ke jagorantar wannan kungiya Kuma ya hannunta Kayan ga Saminu Gajam kamar yanda mai gayya ya bayar da umurni.
WATA DABAN....
P,A na Kwamishinan Ilimi na Jihar Zamfara Babangida Bazukson ya bada nashi tallafin Bokitin Fenti 3 domin ganin ya rage wani abu daga cikin asarar da Allah ya nufa ta riskeshi.
Rayyanu Mai Kaji Gusau na Kungiyar YAZEED TRUST FUND shima yayi Alkawalin daukar nauyin yin fentin, SAMINU GAJAM dai ya yaba da wannan namijin kokari da GARKUWAN MATASAN GUSAU yayi Tare da Addu,ar Allah ya karo budi Tare da Kariya Daga Makiya
Mai Anguwa ma yabawa LAMIDON TSAFE tare da addu'ar Allah ya kaishi inda bai yi tunani ba.
Comments
Post a Comment