JANYAU YOUTH INITIATIVE FORUM



A yau 07/04/2020 wannan kungiyar mai suna a sama, kungiyar matasa ce zallah. Su kansu sun samu kyautar tallafin YARA MASU DARAJA wanda Yazeed Trust Fund ta basu Form 10 domin su ba Yara marayu inji Yazeed shehu Danfulani da nufin zai dauki nauyin karatunsu da kayan karatu kyauta karkashin Gidauniyar Yazeed Trust Fund, ta Hon Alh Yazeed Shehu Ɗanfulani Maidoya Gusau.



Idan dai mai karatu yana biye da mu, faɗi tashin wannan gidauniyar bayar da tallafi da gudunmuwa ta kowace fuska, domin ganin jihar Zamfara ta zarce tsara kuma tayi goyayya da sauran takwarorinta wajan bayar da ilimi mai nagarta a cikin al'umma.


Yana daga cikin kudurin Yazeed ganin ya yaƙi ragaita da yawon ta zubar ga yara masu Daraja, ilimin yaro tamkar zane ne a saman dutsi, wannan ne yasa wannan bawan Allah yake kokarin bayar da kowace irin gudunmuwa ga Yara musamman Marayu da marasa gata akan Rashin zuwa makaranta saboda rauni, da kuma talaunci.

A lokacin miƙa wannan forms ta hannun Comrd Rufa'i Bala UB Gusau Kungiyar waɗannan matasa sun yi murna sosai da samun wannan tallafi ga iyalansu, da 'yan uwansu da kannensu. A ƙarshe sun yi jinjina haɗi da addu'a da fatan alheri ga wannan Gidauniya da kuma masu dafe mata baya.


Daga Nura Mai Apple

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’