KUNGIYAR RAJIN CI GABAN MATA A TUDUN WADA GUSAU


.

Sun bukaci hada karfi da karfe da Gidauniyar Yazeed Trust Fund don Suma su zama jakadun amfanar da al'umma, irin yadda wannan gidauniya ke taimako shi ne ya janyo hankalin wannan kungiya domin ganin an tafi tare, domin ciyar da jihar gaba.


Wannan kungiya mai rajin ci gaban Mata da ke Tudun Wada Gusau, sun gayyato Gidauniyar YAZEED TRUST FUND karkashin Jagorancin (Comrade Rufa'i Bala UB Salanken Galadima) inda suka nuna bukatuwarsu akan son Suma su zama jakadun (Yazeed Shehu Danfulani Lamidon Tsafe, Garkuwan Matasan Gusau) lura da yadda ya keta kokarin taimakon al'umma musamman kananan Yara, Mata, da kuma marayu.

Shugabar Matan (Hajiya Kulu) ta bayyana (Yazeed Shehu Danfulani) a matsayin baiwa daga Allah,wanda ta ce ta daɗe tana cin karo da abubuwan alheransa ka ma daga ciyarwa a Asibitota, daukar nauyin majinyata, kula da marayu da bada tallafin waken suya ga mata, shi yasa tabi diddigin sai ta jawo alherin ga jama'arta domin burinta taimakon al'umma.

Shugaban Yazeed Trust Fund Rufai Ub Gusau ya bayyana jin daɗinsa ganin yadda ya samu Abokan tafiya irin waɗanda Yazeed shehu Danfulani ke buƙata domin baida burin daya wuce ci gaban al'umma da taimakawa Mai Rauni da mai ƙaramin ƙarfi.

 A ƙarshe tayi addu'ar Allah ya sanya alaƙar albarka ya karfafamu da Yazeed shehu Danfulani.

Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’