An gayyaci Yazeed Trust Fund domin kallon wasan sada zumunci




Wasan sada zumunci  da aka gayyaci Gidauniyar Yazeed Trust Fund domin  shedarwa, ya ƙayatar.


A kokarin ganin an samar da dangantaka mai dorewa a tsakanin matasa a sassa daban-daba, wannan yasa kungiyaoyin wasan kallon ƙafa na Matasan gada biyu a cikin Gusau, wadannan kungiyoyin biyu sun gudanar da wasan sada zumunci domin kara karfafa dangantaka a tsakani.

Wasan wanda ya gudana a jiya litinin ya kayatar sosai, a lokacin da wannan wasar ke gudana, Shugaban gidauniyar Yazeed Trust Fund (Alh, Yazeed Shehu Danfulani, garkuwan Matasan Gusau, Lamidon Tsafe) wanda ke karkashin kulawar Comrd Rufa'i UB Gusau, tare da 'yan tawagarsa sun samu zuwa wajan, sun kalli yadda wannan wasa ya gudana.

Comrade Rufa'a UB yace wannan gidauniya a shirye take wajan ganin ta hada ƙan waɗannan ƙungoyin wasanni na matasa a yankin, a lokacin bukukuwan sallah masu zuwa. Sannan kungiyar ta shedar da cewar, zata bayar da rigunan wasa, kyauta domin ganin an inganta wasar.

A kullum babban burinmu shine ganin cigaban matasanmu, a cewa Comrade UB,

muna fatan Allah ya cigaba da daukaka wannan bawan Allah da masu son ganin ya ci gaba, ta kowane fanni.


Comments

Popular posts from this blog

Babban burinmu a wannan shekara ta 2020

Zaben 2019: Kungiyar Kabilar Ibo Ta Gindaya Wa Shugaba Buhari Sharadi Mai sauri

Nigeria: ‘Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman’