KUNGIYAR TSAFTACCE KAFOFIN SADARWA NA ZAMANI!
ko shakka babu, samun irin wannan kungiya a Arewacin Najeriya babban abun alfahari ne da sambarka, idan mukayi la'akari da irin karnin da halin da muke a yanzu. Soshiyal Mediya, wata hanya ce ta saurin isar da sako a cikin al'umma ba tare da an wahala ba kamar yadda aka shawo ta a shekarun baya, hanya ce wadda aka samar ta fuskar kimiyya da fasaha. Tabbas Mediya wata hanya ce wadda ya kamata muyi amfani da ita ta hanyoyi nagartattu, hakan zai matukar bamu damar da zamu jefi tsuntsu biyu da dutse daya!
To sai dai kash! Yanzu wasu sun dauki wannan hanya a matsayin wajan sheke aya, ta fuskar cin mutunci, cin zarafi, kyara, tsangwama, damfara, da sauransu. Wani babban abun takaici shi ne; yadda za kaga, yaro yana cin zarafin sa'ar mahaifinsa, wanda kuma wannan ya sha bambam da yadda su wadanda sunka kirkiri manhajojin suke amfani da shi. me ya kaimu haka?
Idan muka dubi irin taruruka daban-daban da akasha yi a wurare daban-daban domin wayar da kai, hadi da yin kira akan illar dake tattare ta fuskar watsa labaran karya, har yanzu wasu daga cikin al'ummarmu sun yi biris da wannan lamari kiranye.
Babu yadda za'ayi ka shirya labarin soki-burutsu ka rubuta sannan ka wallafa, kuma kace za'a zauna lafiya, hakan ba zai samu ba, wannan haka yake ko shakka babu!
Yaɗa labarai barkatai, marasa tsari babban hatsari ne a cikin al'umma domin wani lokaci ya kan ƙulla gaba da husuma, da fadace-fadace a tsakanin al'umma, musamman masu bambancin ra'ayi ko yare ko ƙabila ko jinsi, to idan mukayi sanadiyar tayar da ƙayar baya, ko menene ribarmu? Shin ko muna amfanuwa da wani abu ta sanadiyar haka? To in kuwa haka ne, me zai hana muyi amfani da hikimarmu da kwarewarmu wajan sadar da alheri domin samun rahama a wajan Ubangiji. Yana da kyau mu dawo saman turba managarciyya.
Mun yaba da kafa wannan kungiya;
tun lokacin da nayi araba da wannan kungiya nace to anzo wajan! Yunkurin samar da kungiyar tsaftacce Mediya (media) abu ne mai kyau, kuma idan aka tsaya aka jajirce za'a samu dukkan nasarar da ake bukata ta wannan haujin. Duk da kasancewar a kungiyance bansan ko akwai daftarin tsare-tsare ba, amma ina son nayi amfani da wannan damar domin bayar da tawa 'yar shawarar don ganin wannan kungiya mai albarka ta samu cigaba ta kowane fanni a matsayina na daya daga cikin 'ya'yan wannan kungiya mai albarka.
1 akwai bukatar tun da wannan lamarine wanda ya shafi al'umma mabambanta, ya na da matukar muhimmancin gaske dukkan wanda yake a cikin kungiyar ya kasance a matsayin wakilin kungiyar a duk inda ya tsintsi kansa, sannan ya kasance dukkan 'ya'yan kungiyar za suyi amfani da tsarin dokokin kungiyar wajan gudanar da ayyukansu a cikin kafofin sadarwa.
2 yana da matukar muhimmanci ya kasance kungiyar ta fito da wasu tsaruka a aikace wadanda zasu janyo hankalin al'umma har suji suna da sha'awar shiga wannan kungiyar domin bayar da tasu gudunmuwa wajan yaki da rashin ɗa'a a kafofin sadarwa, da duk wani mai kishin haka.
Daga cikin tsarukan da ya kamata ayi amfani da su akwai; dukkan zaurukan kungiyar mallakar kafar sadarwar WhatsApp ya kasance ana gayyato muhimman mutane masu ilimi akan kafofin sadarwa, a rika tattaunawa da su lokaci zuwa lokaci, domin fede biri har wutsiya a sha'anin amfani da kafofin sadarwa, hakan zai taimaka sosai wajan kwadaitar da 'ya'yan kungiyar dama wasu da ke sha'awar shiga, suji suna son kungiyar.
3 bayan al'umma sun san takamammen manufofin kungiyar, su da kansu zasu so sanin hanyoyin da ya kamata abi wajan samarwa kungiyar da kudaden shiga, a daidai lokaci ne ya kamata kungiya ta bude asusunta, domin fara siyar da fom (forms) a cikin al'ummar da sun kaji suna da ra'ayin shiga.
4 kasancewar kungiyar ta kunshi jihohi daban-daban na Arewa, akwai bukatar kungiyar tayi nazarin fitar da tsarin tattaunawa a kowane mako a cikin zauren whatsApp (Online Meeting every Weeks) hakan zai taimaka wajan rashin dusashewar kungiyar.
5 kungiyar da rika tuntubar masani dokokin kasa, da bayar da ba'asi kan abinda ya shafi illar ketare iyaka wajan yin rubutun ɓatanci ga wani, ko wasu.
6 babu wani abu da za'ayi kuma a samu nasararsa ba tare da an samu hadin kan wadanda sun ka tsaya a turba daya domin kawo sauyi mai alfanu a cikin ba, saboda haka hadin kai shine kashin bayan kaiwa ga kowace irin nasara a rayuwa.
Allah ya taimaki kungiyar Tsaftacce kafofin sadarwa ta Arewa.
Allah ya taimaki shugabannin wannan kungiya masu kokarin samar da cigaba a kowane fanni.
Allah ya taimaki 'ya'yan wannan kungiya mai albarka.
Allah ya taimaki, Arewa.
Allah ya taimaki, Najeriya.
Allah ya taimaki Afrika dama duniyar musulmai kwata!
Daga Nura Mai Apple
Comments
Post a Comment