ME MUKA SHIRYA DOMIN TARBON RAMADAN?
Gidauniyar Yazeed Trust Fund ta shirya wani zama na musamman a ofishin kungiyar dake hannun riga da jifatu a karamar hukumar Gusau jihar Zamfara, anyi wannan zaman ne na taron addu'o'i hadi da nasihohi domin tarbon Azumin watan Ramadan mai falala da albarka.
Kafatanin shugabannin mata na wannan tafiyar ne sun ka shirya wannan zama, inda aka gayyato Malama Maryam 'Na-Inna domin ta bayar da tata gudunmuwa ga matan da suka halarci wannan zama. In da malama, tayi muhimman jawabai daga cikin harda tabo muhimmancin dake akwai wajan bayar da taimako musamman ga marayu, haka kuma ta kwadaitar da irin romon dake cikin wannan wata, a wajan Allah madaukakin Sarki.
Na inna ta ce; ''Manzon Allah (S.A.W) ya yi nuni da 'yan yatsun hannayensa yace; shi da mai kula da maraya suna zo-zo-zo a cikin al'janna''.
Sannan ta kara da cewar; '' tayi murna. Da irin yadda taga wannan kungiyar mai kokarin taimakon Al'umm, babu ko shakka tayi mamakin ace ba'a samun ire-irin wadannan kungiyoyi a cikin unguwanni, domin taimakon al'umma musamman masu dan karamin karfi''.
Watan Ramadan wata ne mai falala wanda Allah madaukakin sarki yake lunka rahama da jinkai ga bayinsa, ko shakka babu yana da kyau mu kara rubanya kokarinmu wajan taimakon 'yan uwa masu dan karamin karfi a cikin al'umma domin rage masu radadin rayuwa.
A cikin jawabinta. Shugaban kwamitin mata, ta Gidauniyar (Alh, Yazeed Shehu Danfulani, garkuwan Matasan Gusau, Lamidon Tsafe) wato Hajiya Maryam Danfuloti tayi jawabin godiya, ga dukkan ilahirin al'ummar da sunka samu damar halartar wannan taro, sannan tayi godiya, ga Malama Maryam a bisa karba goron gayyata na zuwa wannan wajan, tare da bayar da tata gudunmuwa wajan ciyar da al'umma a gaba.
Malama Maryam Na Inna. Malama ce wadda ta shahara wajan koyar da al'umma tarbiyya da kuma sanin ya kamata,, muna fatan Allah ya saka mata da mafificin alheri, ya yiwa zuri'arta albarka.
A nasa jawabin, jagoran tafiyar Gidauniyar Yazeed Trust Fund, (Comrade Rufa'i Bala UB Gusau, shima yayi jinjina da yabo ga dukkan al'ummar da sunka samu damar halartar wannan muhimmin zama da ya gudana. Haka shima kansa yayi tsokaci akan manufar Gidauniyar wajan Daukar nauyin yara marayu zuwa makaranta hadi da dauke masu dukkan wahalhalun rayuwa, inda yace yanzu haka wannan shiri mai taken ''Yara Masu Daraja'' ya nan kuna yana cigaba da yin dubon tsanaki a cikin al'umma, domin zakulo masu dan karamin karfi a cikin al'umma don dauke masu nauyin karatu, tare da kula lafiyarsu.
Haka a ci gaban jawaban na mutane daban-daban a wajan, sun tabo maganar cutar nan mai matukar hatsari a cikin al'umma, kuma mai saurin yaduwa ta Covid19, da kuma hanyoyin da ya kamata al'umma subi wajan kare kansu da kamuwa da wannan cuta, kasancewar hausawa suna cewa Riga Kafi Yafi Magani.
A karshe anyi addu'o'i na musamman na samun zaman lafiya madauwami a jihar Zamfara da Najeriya baki daya
Nura Mai Apple Media Reporter daga Gusau
Comments
Post a Comment